MATSALAR BARA A KASAR HAUSA
Daga
Rabiu Muhammad Abu Hidaya
MA’ANAR KALMAR BARA.
Idan aka ce bara a kalmar hausa.
To ana nufin wani mutum wanda bashi da karfi, wanda yake neman taimako a gurin
mutanen da suka fi shi karfi.
Bara dai ta kasu kashi-kashi.
Misali.
Akwai bara ta yara kanana wadanda ake kawo su daga jihohi gurin malamai domin
neman ilimi.
Akwai kuma bara wadda Makafi da Kutare gami da wasu mutane wadanda suka nakasa
suke yi.
In ka dauke barar da yara wadanda ake kira Almajirai ke yi.
A yanzu muna iya kiran bara ta zama sana’a a kasar hausa.
Idan muka yi duba da yadda Kutare da Makafi kai har ma da wadanda suka samu wata
yar nakasa suka mai da abin sana’a.
Domin za ka ga wani daga cikin Mabaratan a dalilin wannan barar da yake ya gina gida
ya sayi motar da ake masa haya da ita, kamar yadda masu sana’a suke yi.
Amma duk da haka bai dena barar ba saboda ya riga ya maida ita sana’a.
BARA A MIZANIN JIYA.
A lokutan baya bara bata zama abar kyama ba, musamman a yankin Kasar Hausa.
Domin a lokacin da kafin zuwan turawa wajejen karni na sha biyu.
Muna iya kallon bara a wani janibi na dabam misali.
Lokacin muna da sarakuna masu mulki na hakika da malamai wadanda suke
karantarwa yadda yakamata gami da kula da yara cikin mutunci da kamala.
Sannan waccan lokacin ba’a samu yawaitar jama’a kamar na yau ba.
Kuma mutanen waccan lokacin suna da karamci da tausayin wanda bai da shi,
kuma za kaga mabaratan na waccan lokacin ba da son ransu suke yin barar ba. Kuma
da sun samu abinda suke bukata su kan koma muhallinsu.
Wannan yasa wasu mutanen idan suka yi noma a karshen shekara sukan ware wani
kaso su kai wa wadanda suke ganin ba su da karfin da za su iya nomawa kamar kutare,
guragu da makafi.
Wannan tasa wasu daga cikin Nakasassun dena fitowa waje bara domin sun samu
abinda zai wadatar da su.
BARA A YAU
Bara a yau ana iya kiranta wata gagarumar matsala wadda ta dade tana kawo cikas ga
rayuwar ya’yan hausawa.
Misali.
Bari mu fara da yara kasancewar sun fi yawa a cikin bara.
Iyaye kan dauki dansu su kai shi gurin wani mutum wanda yake bada karatu a matsayin
Almajiri (mai neman ilimi) wanda daga nan kuma iyayen sai su manta da rayuwar yaron
basu san cin saba basu san shan sa ba, domin suma talakawane abinda za su ci wuya
yake musu, wasu ma da gangan suke kai yaran Almajiranci domin gidajen da suke
kwana ya yi musu kadan kuma ga abincin da yake kawowa baya isar su ga yara an
hayayyafa da yawa to daga nan sai kaga uba ya dauki dansa ya kai shi can wani gari
mai nisa wai da nufin karatu ya kai shi.
Wasu iyayen su kan ce kada a bar yaro ya taho ganin gida har sai ya sauke su kuma
daga nan sai sun kai wajen shekara guda da rabi ba su sake waiwayar sa ba, daga nan
sai su kulle dan abinda bai kai ya kawo ba su kai wa malamin da yaron nasu a madadin
ladan kula da yaron su da yake yi.
Wanda shi kuma malamin shi ma talauci yana damunsa gashi kuma babu wata
kwakkwarar sana’a da ya dogara da ita, kuma gashi an tara masa yara gurinsa kuma
iyayensu sun yi nisa da su.
Sai kaga bai da lokacin tarbiyar ko wani yaro kuma bai damu da halin da yara za su
shiga ba,
Idan damina ta fadi wasu malaman kan dauki wadannan Almajiran nasu su ta fi dasu
wani gari domin su yi wa Mutane Noma a biya su.
Yawanci wannan kudi da ake samu malaman ne kan sanya su a cikin aljihunsu, kuma ba
su fiya damuwa da irin rayuwa da yaran kan kasance a ciki ba.
A halin da ake ciki a yau irin wadannan yara da ke kawowa Almajirci za ka dinga ganinsu
wajen yan tuwo-tuwo da gurin Yan daudu gami da yin sana’ar Bola-bola(Gwangwan)
daga nan sai kaga sun shiga shaye-shayen kananan kayen maye, irinsu Sholiso Madarar
Suku dayin.
Domin guraren da suke ziyarta gurarene na matattarar masu irin wadannan dabi’u.
Yawanci malaman basa farga sai abin ya yi nisa domin yawan Almajiran da ke garesu
gashi kuma iyayensu sun yi nisa da su balle har su san yanayin rayuwar ya’yansu shima
kuma Malamin ga nashi Ya’yan ka ga da wan ne zai ji kenan?, dan haka da an tashi daga
karatu bai damu da gurin da kowa zai je ba.
Wasu yaran daga nan sai su balle daga makarantar su dena zuwa su koma can tasha da
Matattarar yan Bola-bola su cigaba da zama.
Lokaci-lokaci su kan bullo makarantar su baiwa malaman nasu dan ihsani(wasu yan
kudade ko kaya) gami da sanar da ai suna nan aiki suka samu.
Su kuma malaman kan karba gami da yi musu wasu yan nasihohi.
Idan muka kalli samuwar wannan matsala za mu ga bara ce ta haifar da ita domin da
yaron bai je ba da ba zai samu damar fita bara ba balle har yasan irin wadannan gurare.
Kuma yawanci irin illar da wadannan yara ke haifarwa tana da yawa ga kasa, domin
basu samu cikakken ilimin da ake so su samu ba.
Gashi kuma ba su samu kyakkyawar tarbiya ba, hakanan sun yi biyu babu domin babu
cikakken ilimin Addinin babu na zamanin sai kaga yaro ya tashi cikin rashin tausayi
haka kuma yawanci irin wadannan yara basu fiye komawa garuruwansu ba.
Kaga an bata goma biyar bata gyaru ba.
Idan muka dawo bangaren manya kuma za mu ga yadda a yau suka mai da bara sana’a
kai har ta kai ma da wanda ya nakasa da wanda bai nakasa ba duk bara suke.
Matsalar da wannan barar take hai far yana da yawa na farko.
a.Mutuwar Zuciya.
b.Hassada da gaba.
c.Rashin Wadatar Zuci.
Bari mu fara dana farko wato mutuwar zuciya.
Idan ya zama yau a baka gobe a baka to zuciyar takan mutu wajen yin tunanin hanyar
da zaka yi wata sana’a dan dogaro da kanka.
Hassada da gaba.
Hassada da gaba takan shiga tsakanin mabaraci da masu bayarwa, domin duk lokacin
da ya zo ya yi bara baka bashi ba haushinka ya ke ji tare da bakin ciki dangane abinda
kake da shi.
Rashin wadatar zuci.
Irin wadannan mabarata kan tara dukiya ta hanyar bara, amma kullum zaka gansu jiya i
yau. Babu wanka balle kyakkyawar sutura.