Dalilan Mu Da Suka Gayyatar Buhari Majalisa – Yakubu Dogara

0

Kakakin Majalisar Wakilan Najeriya ya yi karin haske kan dalilan da suka sa majalisar ta bukaci Shugaba Muhammadu Buhari ya bayyana a gabanta domin ya yi wa majalisar bayani kan yawan kashe-kashen jama’ar da ake yi a fadin kasar.

Yakubu Dogara ya wallafa a shafinsa na Twitter cewa hakkin gwamnati ne ta samar da tsaro ga al’ummarta, a don haka majalisar “ba za ta zuba ido tana gani ana kashe jama’a ba”.

Wannan matakin da majalisar ta dauka ya biyo bayan bukatar da dan majalisa Mark Gbilah daga jihar Benue ya gabatar a  zauren majalisar, inda aka kashe mutum 17 tare da wasu limaman coci biyu ranar Litinin da ta gabata ne.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here