An Sake Kashe Sama Da Mutum 25 Da Kona Masallatai A Benue

0

Rahotanni sun ce akalla sama da mutum 25 ne aka kashe, yayin da wasu da dama suka jikkata a rikici na baya-bayan nan a Makurdi, babban birnin jihar Benue.

An kuma kona masallatai da kuma hasarar dukiya a harin wanda ake zargin na ramuwar gayya ne da ake zargin ‘yan kabilar Tivi da kai wa Hausawa ko kuma Musulman jihar.

A tsakanin ranar Lahadi zuwa jiya Alhamis an kashe akalla mutane 78, kamar yadda wani basarake daga  karamar hukumar Logo Joseph Anawah ya bayyanawa manema labarai cewa a yankinsa an tsinci gawar mutane bakwai wadanda  suke maza da mata da kuma yara.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here