BARABO DA GWANIBA

0

BARABO DA GWANIBA

From Umar Cikingida
Allahu akbar shekara kwanace yau 1 ga April 2018 ne ya Marigayi Malam MDyusufu ya cika shekaru ukku da rabuwa da ku amma haryanzu jimamin rashin shi.
A cikin abubuwan alkhairi da zamu iya tunashi da su sune:
Kamar Katsina Vocational Training Centre, wannan cibiya marigayi ne ya kafata run shekarar 2000 Wadda ya hannan ta amarta a hannun Hazikin danjarida, marubuci, kuma masanin Al amurran yau da kullun Watauga Muhammad Danjuma Katsina. Wannan kungiya ta horas sales sama da matasa 10,000 sana’oi daban da ban kuma abun burgewa anan duk wannan horon kyautane kuma harda kudin matsin yake badawa ga masu karatun duk wata. Wani abun burgewa ga mai karatu shine har Yanzu da Muke shekaru 3 bayan rashuwarsa babu abunda ya tsaya a cikin cibiyar.
Nabiyun su shine wata Cibiya da ya bada umarnin Kafawa da buncike Watauga (MDyusufu Research and Documentation Centre) Wadda Allah bai nufi ya ga aza harsashen ginin ta da kanshiba amma ita ma wannan wuri ya damka alhakinsa a hannun amintattun mutane. Alh Ibrahim Coomasie shine shugaba, Wanda Marigayi Alh. Umaru Shinkafi yake MA mataimaki, sai kuma Muhammad Danjuma Katsina shine sakataren wannan katafaren aikin. Wannan aiki ya zuwa Yanzu duk shirye shiryen sa sun kammala, barcin da wannan rashe rashen da suka faru na shi Marigayi Alh MDyusufu da Alh Umaru Shinkafi da tuni aikin ya kammala, amma yanzu komai ya daidaita ana gab da farawa Kamar yadda sakataren su ya shaida mani.
Daga cikin abubuwan akwai yadda yake bada gudumuwa wurin aikin Allah, ba zan mantaba lokacin rasuwar cikin wadanda suka zo gaisuwa akwai babbar tawaga daga Kaulaha Wadda Limamin Babban Masallaci Shehu Ibrahim Inyass ya jagoranta, ina wani daga cikin su ya shaida mani cewa duk fadin Africa babu wanda ya Kaishi bada gudumuwa yayi ginin Masallacin.
Da fatan Allah ya sanya wannan aiyukan Alkhairi Su Zamo daga cikin kyawawan ayyukan da za’ayi mashi awon mizani da su. Amin

See also  Wannan Shine Sheikh Sharifideen. Anhaifeshi A Shekarar 1993 Garin Swahili Cikin Wani Coci Da Ake Kira Katolic

Umar Cikingida
Chikingida@yahoo.com
08020607662

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here