YADDA AKA KIFAR DA GWAMNATIN BUHARI A 1984

0

YADDA AKA KIFAR DA GWAMNATIN BUHARI A 1984

A jiya Asabar ne aka kaddamar da littafin tarihin Rayuwar sarkin gwandu… Muhammad Bashir..taron ya samu halartar jiga jigai a kasar nan ..cikinsu har da wakilan shugaban kasa .. Wanda gwamnan Katsina Alhaji​Aminu Bello Masari cfr ya wakilta..
Wani babi da yafi daukar hankali a littafin shine..na Inda sarkin gwandu ya bayyana dalla dalla kuma Daki daki yadda..aka kifar da gwamnatin Buhari a 1984.

Labarin da ke a wannan babin Yana da jan hankali da darasi sosai..shi yasa wakilin mu na musamman.. Abdurahaman Aliyu ya fassara Mana..shi..kuma zamu dau .. lokaci hudu muna gutsuro shi… karanta kaji. Yadda akayi wasa da kwalwa….

Asha karatu lafiya

YADDA AKA KIFAR DA GWAMNATIN BUHARI A 1984

Fitowa ta daya..

Tun Bayan da aka cire mai martaba Sarkin Gwandu na 19 Alhaji Mustapha Jakolo aka maye gurbinsa da Alhgaji Muhammadu Ilyasu Bashar, wanda aka fi sani da Manjo Janaral Muhammadu Jega, yakin cacar baki ya balla tsakanin Sarakunan biyu, wanda ya haifar da mayar da murtani akan al’ammura da dama da suka shafi masarautar da kuma zamantakewa ta yau da kullum.
Jakolo ya mayar da raddi a kan wani littafi da mai Martaba Sarkin Gwandu Alhaji Muhammadu Ilyas Bashir ya rubuta wanda ya yi bayanin yadda Muhammadu Buhari ya samu mulki a shekarar 1983.
Kasancewa shi Sarkin ya na daya daga cikin manyan sojiji a wancen lokacin.

Wannna littafi shi ne na farko da wani babban soja ya rubuta wanda yake da masaniya kan abin da ya faru Nijeriya sannan ya kawo bayanin abin da ya faru a Inugu da Kano da Kaduna Lagos da abin da ya faru kan rasa rayuka ‘yan kabilar Igbo sama da dari shidda a lokacin. Sannna ya yi bayani dalilan da suka haddasa yiwa Shehu Shagari Juyin Mulki da kuma abubuwan da suka kai ga darewar Muhammadu Buhari a kan Mulki a 1983, kasancewarsa fitacce kuma daya daga cikin manyan sojoji a lokaci da aka fi saninsa da sunan (MD Jega).
Sannan a cikin littafin ya yi bayanin yadda Buhari ya zargi Janaral Ali Gusau kan batun lasin shigowa da kaya a qasar nan, wanda hakan ya sa ya tara makudaden kudade, wadanda da su ne aka dauki nauyin juyin mulkin da aka yiwa Shagari. Wanda ya kai Muhammadu Buhari bi sa mulki, wannan abun ne ya sa da yawan mutane ke zargin Muhammadu Buhari kan yadda ya nemi ya kori Janarl Ali Gusau daga mulki, cikakka bayanin yadda abun ya faru yana cikin littafin da mai Martaba sarkin Gwandu Alhaji Muhammad Ilyasu ya rubuta.

Jakolo ya kalubalanci abubuwa da yawa da ke cikin wannnan littafin a wata hira da aka yi da shi a jaridar SUN ya bayyana cewa.
Tsohon Mai baiwa Shugaban Kasa Shawara a Harkokin Tsaro, Sambo Dasuki, da ke a tsare yanzu, shi ne ya shirya tsare-tsare kuma ya dauki nauyin yadda aka aiwatar da juyin mulkin 1983, wanda Muhammadu Buhari ya zama shugaban kasa na mulkin soja.
Jakolo, wanda shi ne sarkin Gwandu da aka tube wa rawani, shi ne ya yi wannan ikirari a cikin raddi da yayi wa littafi da Janar Muhammadu Bashar mai ritaya ya wallafa.
Ya ce a lokacin Dasuki ya na Manjo, shi ne ya rika fadi-tashin nemo kudaden da aka shirya yadda za a dora Buhari kan mulki a matsayin shugaban mulkin soja idan an yi wa Shugaban Kasa na lokacin, Shehu Shagari juyin mulki.
Jakolo yace idan dai ana batun juyin mulkin 1983 ne, to “zance na gaskiya dalili ke nan na ke yin kukan zuci a yanzu, idan ina tunanin halin da Sambo Dasuki ke ciki a yanzu. Abin ya na damu na.
“Haka al’amari ke jirkitawa. Idan da ban shigo da Dasuki a cikin shirya juyin mulkin ba, to da batun ma Buhari ya zama shugaba na mulkin soja bai ma taso ba. Sambo ne ya yi ruwa, ya yi tsaki ya ce lallai sai Buhari, ni kuma na goyi bayan sa.
“Na rantse da girman Allah (SWT) Sambo ne ya tsaya kai da fata ya ce sai Buhari.
Ni kuma na hada su da Dasuki, kai ko a lokacin da mu ke tsara juyin mulkin, shi ne ke karbo mana kudade wurin Aliyu Gusau, da Hafsan Hafsoshin Sojoji ya taimaka wa juyin mulkin, saboda ba mu samu ko sisi daga Buhari ba.
“Kai Sambo Dasuki bai tsaya a nan ba, sai da ya yi amfani da kudin sa, ya dauki nauyin wasu malamai zuwa Saudi Arebiya su ka yi addu’o’i a Ka’aba domin juyin mulkin ya yi nasara.”

Kamar yadda aka rawaito a littafin Gwamnatin Buhari ta fara ne cikin matsanancin yanayi, wanda ya hada da yaki da cin hanci da rashawa da daure barayin da suka saci kudin gwamnati da kuma kalubalen wasu manyan Sojoji da ke kawowa gwamnatin Barazana wajen tafiyar da ayyukanta.

Wannan yasa gwamnatin Buhari ta sa ayi bincike karkashin jagorancin Birgediya Gada Nasko kan masu shigowa da kaya daga kasar waje lokacin mulkin Shagari, kwamitin ya samu hannun Janar Ali Gusau dumu-dumu a ciki, maganar lasisi, na shigo da kaya daga waje, Janar Gusau ya fadawa Kwamitin cewa Janar Babangida na da masaniya a kan wannan maganar Lasisi. Lawal Rafin Dadi daraktan Hukumar Tsaro ta kasa wadda yan zu ta koma SSS shi ne shugaban kwamitin dake bincike bangaren sojoji bai kira Janar Babangida ba, domin tuhumar da ake yiwa Janar Gusau. Wannan ya sa janar Ali Gusau ya tafi wata makaranta mai suna Royal College Defese Studies domin ya halarci wani kwas.
Wannan ne ya bada dama ga Rafindadi ya gudanar da bincikensa cikin tsanaki, daga karshe dai kwamitin ya samu Janar Ali Gusau da hannu dumu-dumu kan maganar lasisin. Rafindadi ya yi farinciki da wannan abu kuma ya yanke hukuncin sanar da Shugaban kasa Muhammad Buhari domin daukar matakin da ya dace.
Buhari ya yanke hukuncin cewar a kori Ali Gusau daga aiki saboda an same shi da laifi, amma wasu jami’an soja suka ki yarda da wannan mataki, shi kuma Buhari ya tsaya kai da fata lallai sai an kori Janaral Gusau daga aiki. Duk da cewa a daidai lokacin gusau ba ya kasar yana cen yana kos.
Sannan sojoji da yawa sun ba Buhari shawara kar ya kori Janarl Ali Gusau, musamman saboda rawar da ya taka wajen hawansa mulki.

Da abu ya yi kamari aka nemi Janaral MD Jega da ya shiga tsakanin domin samu daidaito, amma shi kuma ya sa shakku na shiga tsakanin Shugaban kasa da Majalissar Koli ta Soji.
Saboda su majalissar koli basu goyan bayan a kori Janar Ali Gusau daga aiki. Amma shugaban kasa ya cije lallai sai an kori Gusau ya bayar da dama ga hukumar DIA da su zartar da hi hukuncin lokacin sakataren hukumar Koloniyal Rabi’u Aliyu ya tafi hutu sai aka umurci mataimakin shi Lutanar Kwaloniya Bashir Salihi Magashi da ya zartar da kudirin.

Wannan kudirin ya tsorata manya sojoji da ke a majilissar Koli inda suka shiga taitayinsu, wanda hakan yasa har Manjo Janar Ibrahim Babangida ya yi niyyar yin ritaya da aiki, saboda rade-radin da suke samu na ciresu da za a yi daga aiki.
Wanda a lokacin Janar Babangida ya yi niyyar tafiya hutu, amma sai ya samu jita-jitar cewa da ya tafi za a maye gurbinsa da Muhammadu Magoro ko kuma Gado Nasko.

Wannan yunkuri ya tayar da hankalin da yawa daga cikin Sojojin Majalissar koli ta kasa, musamman ma wadanda ke da hannu a juyin mulkin da aka yiwa Shagari.

Littafin ya hakalto cewa wannan takun saka ya sa Janar Babangida ya fara ja da baya ga gwamnatin Buhari.
Duk wadannan abubuwan da ke faruwa She M D Jega a tsakiya ya ke bai goyan bayan kowa da ga cikin su.
Bayan Shugaba Buhari ya sa ke bada damar a Binciki Janar Babangida kan wasu almundahanar kudade da suka taso a Majalissar Koli ta soja. Kamar yadda aka rawaito a cikin littafin an ce Janar Babangida ya samu jita-jitar wannan labari daga wajen wasu yaransa na shirin bincikarsa da ake shirin yi.
Jega ya bayyana cewa a kan wannan matsalar sai da ya shawarci Buhari da abi hanyar Difilomasiyya wajen warware matsalar, amma Buhari bai dauki shawarar ba.

Littafin ya yi bayani sosai kan Matsalolin da suka haddasa kifar da gwamnatin Buhari a wancen lokacin. Wadannan matsaloli dai su ne wadanda suka faru tsakanin Janar Buhari da Janar Babangida da wasu manyan hafsan sojojin a Majalissar koli ta soja.
Tun lokacin da Janar Babangida yake matsayin na uku a Kasa ya ke da yara kwararru wadanda ya ke taimakamawa, kuma suke mashi biyayya kwarai da gaske . Wanda hakan ya ba da dama ga Janar Babangida wajen shirya juyin Mulki cikin sauki.

Wata karin damar kamar yadda aka hakalto a littafin ita ce kokarin korar Janar Ali Gusau daga aiki duk da rawar da ya taka wajen ganin Janaral Buhari ya hau mulki.
Wannan dalilan suka sanya gwamnatin Janar Buhari ta sanya ido ga duk wani motsi na Janar Babangida da Janar Ali Gusau a karkashin hukumar leken asiri ta kasa ta hannun Lawal Rafindadi. Har ta kai duk wayoyin da za su buga ana sanya masu ido dan ganin motsinsu.

Littafin ya yi bayanin yadda aka nada Koloniyal Halliru Dakiku a matsayin Darakta na daya a hukumar Leken Asiri ta kasa bayan da aka tura Lutanar M.C Alli Ingila domin karin samun horo.

A dai-dai wannan lokaci Janar Babangida da Janar Abacha da wasu manyan Hafsoshin Soji fara zaman sirri na yadda za su hambarar da gwamnatin Janar Buhari, an yi zaman a Legas da Minna da kuma Landon.

A Minna in da nan ne Mahaifar Janar Babangida, gwamnan soja na lokacin Lutanar Kanal David Mark ya ba shirin na juyin Mulki kulawa ta musamman in da ya bayar da wurin da aka rika tattaunawa da tsara yadda za a gudanar da juyin Mulkin. Jagoran juyin Mulki a Minna shi ne, Laftanar Kanal Tunji Olurin.

Shugaban tsara wannan juyin Mulki Janar Babangida ya rika neman goyan baya ga sauran ‘yan kasa cikin sirri wadanda suka hada da, Shahararrun ‘Yan kasuwa da fitattun ‘yan jarida da Malaman manyan makarantun gaba da sakandire da wasu Malaman addini. Sannan ya nemi hadin kan wadanda Janar Buhari ya taba ta fuskoki da dama musamman ‘yan kasuwa wadanda suka hada da:

Alasan Dantata, Kano da Isyaka Rabi’u, Kano da Ahmed Maidarbe, Maiduguri da Baki Kwanta hira, Neja da Tsoho Dan Amali, Sokoto da Haruna Danji daga Zaria da sauransu da wadanda aka Zarga da yiwa tattalin arzikin kasa zagon kasa.

Littafin ya bayyana wasu fitattun Mutane da gwamnatin Janar Buhari ta yi takun saka da su, wadanda suna daga cikin abin da ya taimaka wajen durkushewar gwamnatin. Daga cikin su akwai Abubakar Gumi da da Obafemi Awolowo.
Cire Abubakar Gumi daga shugaban hukumar Alhazai da dakatar da Albashinsa tare karbe motar ofishinsa na daga cikin kuskuren ko kuma wani abu da ya kara kawowa gwamnatin koma baya.
Shi ma a nasa Bangaren Awolowo an aika motar sojoji sun zagaye gusansa dake Park Line a Apapa, ba tare da lura da abin da hakan zai haifarba, irin wadannan abubuwan su suka sanya juyin mulkin ya samu karbuwa a zukatan wadanda ake tuntubar.

Duk wadannan abubuwa da ke faruwa na shire-shiren hambarar da gwamnatin Janaral Buhari, ya samu labari ko kuma ya ji jita-jitar faruwar hakan. Amma kuma sai bai dauki wani mataki ba na magance faruwar Hakan.
Shahararren Dankasuwar nan M.K.O Abiyola shi ma ya taimaka wajen bayar da gudumuwar kudi domin hambarar da gwamnatin Janar Buhari duk da cewa ya taimaka kwarai wajen darewar Buhari bisa shugabancin kasar nan a 1983, amma gwamnatin Buhari ta Munana masa musamman da ta amshe mai tarin kaya kuma ta yi gwanjonsu ga ‘yan kasa.
Littafin ya bayyana yada jagororin juyin mulkin suka zauna suka tsara yadda abin zai kasance musamman ma in an yi nasara, kamar yadda ake yi dai a ko wane irin juyin Mulki.

Littafin ya hakalto irin matsalar da aka samu tsakanin Janar Buhari da jagororin da suka tsara juyin Mulkin, a cikin littafin an bayyana yadda jagororin juyin mulkin suka shirya yadda za su damke Janar Buhari cikin tsakar dare ba tare da fuskanta wata matsala ba wadda zata haddasa zubar da jini. Sannan an tsara yadda za a magance duk wani wanda ake tunanin zai iya bada matsala ga juyin mulkin.

Juyin mulkin ya yi shakulotin bangaren da wasu manyan jami’an Soji wadanda suka hada da:
Manjo Janar M.D Jega da Gwamnan Gongola Muhammad Magoro da Ministan harkokin cikin gida da wasu tsirarun Hafsoshin Soji a lokacin.
A cikin littafin an zayyana sunayen Sojojin da suke da sa hannu waje tsara wannan juyin Mulki wadanda suka hada da:
1. Janar Ibrahim Badamasi Babangida
2. Birgediya Sani Abacha
3. Koloniyal Joshua Dogon Yari
4.Koloniyal Aliyu Muhammad Gusau
5. Laftanar Kanal Halliru Dakiku
6. Laftanar Kanal Tunji Ayuba
7.Laftanar Kanal David Mark
8. Laftanar Kanal John Shafeta
9. Laftanar Christ Abuta Garba
10. Laftanar Kanal Raji A Rayaku
11. Koloniyal Anthony Ukpo
12. Manjo John Madaki
13. Manjo Abdulmumini Aminu
14. Manjo Lawal Gwadabe
15. Manjo Abubakar Dangiwa Umar
16.Manjo Sambo Dasuki
17. Manjo Maxwell Khobe
18. Manjo UK Bello
19. Manjo Kapas H. Bulus
20. Kaftin Nuhu Umar
21. Kaftin Suke Ahmad
22. Kaftin Musa Shehu
23. Laftanar Kanal Ahmed Daku
24. Laftanar Kanal Abubakar Dada
25. Manjo I.B Tsoho
26. Manjo Friday Ichidi
27. Kaftin M.Bishir
28. Manjo S.P Mepalyede

Akwai kuma Sojojin da suke da masaniya kan juyin Mulkin amma ba su taka wata rawa ba wajen gudanar da shi, da ga cikin su akwai;

1. Birgediya Peter Ademokhi
2. Birgediya Abdullahi Bagudu Mamman
3. Birgediya Y.Y Kure
4. Birgediya Ola Oni
5. Lutanar Kanal John Inieger
6. Lutanar Kanal Tunji Olorin
7. Lutanar Kanal A. Abubakar
8. Birgediya Garba Duba
9. Ike S Nwachikwu
10. Jeremiah T Useni.

Haka kuma littafin ya rawaito sunayen wadanda suke bayan gwamnatin Buhari a ya yin juyin Mulki, da ga cikinsu akwai:

1. Manjo Janar M.D Jega
2. Mamman Vatsa
3. Muhammad Magoro
4. Muhammad Lawal Rafindadi
5.Laftanar Kanal Sabo Aliyu
6. Birgediya Salihu Ibrahim
7. Manjo Mustapha Jakolo.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here