Shugaba Buhari Ya Gana Da Donald Trump

0

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya gana da takwaransa na Amurka Donald Trump a fadar White House da ke Washington a yau Litinin.

Shugabbannin sun tattaunawa kan batutuwan tattalin arziki da tsaro da suka shafi kasashen biyu.

Muhammadu Buhari ya zamo shugaba na farko daga nahiyar Afirka (Kudu da sahara) da ya gana da Mista Trump a Washington.

Amurka da Najeriya na da alaka ta kut-da-kut wacce suka shafe shekara da shekaru suna martaba wa.

Shugaba Buhari ya gana da manema labarai inda ya amsa wasu tambayoyi da suka shafi harkar tsaro da kuma yaqi da ya ke dacin hanci da rashawa.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here