YADDA AKA KIFAR DA GWAMNATIN BUHARI A 1985

0

YADDA AKA KIFAR DA GWAMNATIN BUHARI A 1985

Fitowa ta Biyu

Littafin ya rawaito cewa, jita-jitar gudanar da wannan juyin mulki, ta karede kasa. Wannan jita-jita an yin ta ne ga wadanda suke da masaniyar yadda za ayi juyin mulkin, wanda aka tsara ta amfani da basira da kwarewa, wanda duk kwarewa da kuma bajintar jami’an da ke tattare da  Buhari a lokcin sun gaza gane ta inda kullin yake.

A karshen watan Yuni na shekarar 1985 tuni wadanda suka shirya juyin mulkin suka samu nasarar darsa jita-jitar juyin mulkin a zukatan wasu makusanta Buhari. Marubucin littafin ya ruwaito cewa a dadai wannna lokaci Alex  Ibru ya samu labarin yadda Babangida yake qullawa gwamnatin Buhari da Idiagbo qulalliya.

Wannan ya sa Ibru ya samu Koloniyal M.C Alli, wanda a lokacin shi ne mukadashin darakta na hukumar bincike ta soja. M.C Alli ya shawarci Ibru da cewa su tafi kawai su samu Idiagbo  a gida su sanar da shi halin da ake ciki. Amma abin mamaki sai Idiagbon ya ki amincewa da wannan zance da su ka zo mashi da shi, ya tabbatar masu da cewa babu abin da zai faru.

Haka jita-jitar wannan juyin mulki ta karade kasa, wanda su wadanda suka tsara juyin mulkin suka haddasa. Wannan ya jawo hanalin majalissar koli ta kasa kan wannan yunkuri na juyin mulki. Daga qarshe ma Daraktan hukumar bincike ta kasa ya sa a tsare Koloniyal Tanko Ayuba bisa zargin haddasa jita-jita da kuma yunkurin juyin mulkin, amma daga karshe Tanko Ayuba ya bijirewa duk wadannan tuhume-tuhume da ake yi masa, duk da cewa a zahiri ya na tare da masu yunqurin juyin mulkin.

A cikin watan Agusta na 1985 hukumar bincike ta kasa ta kara samun wata jita-jita cewa , Aliyu Gusau ya na shirya wani abu kan ritayar dole da aka yi masa, wanna ya sa, hukumar ta kara tashi tsaye domin ta bayar da kariya ga shugabn qasa Muhammadu Buhari.

A dai-dai wannan lokacin kuma Babangida ya na cen ya na rangadin ganawa da manyan sojoji, da ke fadin kasar nan.

Haka kuma marubucin littafin ya rawaito cewa, a cikin wannan hali ne dai, Koloniyal M.C.Alli wanda ya damu da wannan hali da ake ciki ya sake samun  Idaigbo ya fada mashi cewa yana samun bayanin wannan juyin mulki fa daga duk kusurwowin kasar nan, saboda haka ya kamata a yi wani abu. Amma sai Idiagbo ya gargade shi da cewa ya bar wannan maganar, su basa bukatar duk wani abu da za a zubar da jini.

Ba M.C Alli kadai Su Buhari su ka yiwa gargadi ba kan samun labarin yunkurin kifar da gwamnatinsu, har Mamman Vasta shima da yazo da labarin Babangida na son kifar da gwamnatin sun gargadeshi kan wannan magana. Daga karshe ma sai aka zargi cewa kujerar Babangida yake nema ta Shugaban Sojoji shi ya sa yake wannan abu.

A dai cikin wannan wata na Augusta Shugaba Muhammad Buhari ya sanar da tafiya hutu a mahaifiyarsa Daura. Sannan mataimakinsa Idiagbo tare da Mamman Vatsa da Birgediya Mamman Nasarawa da wani karamin dansa suka tafi Kasar Saudiya domin aikin Hajji.
Sannan kusan kowace Baraki ana zaman dar-dar na garambawul da Gwamnatin Buhari za ta yi a bayan hutun Sallah. Wannan yunkuri ya taimaki kwarai wajen yin sakaki da tsaron kasa, musamman saboda tsoran rasa ayyuka da wasu Sojojin ke yi.

Wannan jita-jita ta sa Babangida ya shiga shakku.

Wanna jita-jita ta jawo hankalin Ministan harkokin Ciniki, Mahmud Tukur, wanda ya je gida a lokacin Yola, sai ya yanke hukuncin Zarcewa gidan Gwamnatin Jihar in da ya samu Gwamnan, Manjo Janar M.D Jega, ya ke sanar da shi cewa akwai takun Saka sosai tsakanin Buhari da Babangida, in da ya bukaci da ya shiga tsakani domin sasantawa.

Jega ya sanar da shi cewar ya na da masaniya kan wannan jita-jita da ake ta yadawa, kuma ya tabbatar wa Mahmud Tukur da cewa zai yi iyakar kokarinsa domin ganin an yi sasanci.
Jega ya yanke hukuncin cin zai kira taron gaggawa idan Idaigbo ya dawo daga Hajji, in da zai zauna da duka bangarorin domin yin sasanci.
Jega ya kira Babangida ta waya in da ya sanar da shi halin da ake ciki, Babangida ya mayar mai da amsa kamar haka, “Mallam kar ka damu, zan zo Yola musamman in ganka bayan Sallah”

Saura Kwana biyu Sallah Murtala Nyako da Aliko da wasu sauran Sojoji sun kai ziyarara Yola domin ganawa da iyali, sun ziyarji Jega in da ya tattauna da su kan abin da ke faruwa, sai dai abin da bai sani ba dukkansu suna da hannu tsundum a yunkurin juyin mulkin.

Zamu cigaba..

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here