Gwamnati Ta Haramta Shan Kodin A Najeriya

0

Gwamnatin Najeriya ta haramta hadawa da sayar da maganin tari mai Kodin bayan BBC ta bankado yadda ake sayar da shi barkatai.

Ministan Lafiya na kasar Farfesa Isaac Adewole ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar ta hannun Mataimakin Daraktan watsa Labara na Ma’aikatar Olajide Oshundun.

Mr Oshundun ya shaida wa manema  labarai cewa za a ci gaba da sayar da wadanda suka rage amma kawai ga wadanda likitoci suka ce a bai wa.

A binciken da BBC ta gunadar ya gano cewar masu safarar kodin suna aiki cikin kamfanonin da ke hada maganin, kuma suna sayar da magungunan ba bisa ka’ida ba.

See also  Matashi ya hallaka kawun sa kan zargin maita.

Miliyoyin matasa a Najeriya na shan maganin, wanda ke sa mutum ya nace masa, domin su bugu.

Maimakon amfani da kodin, ministan ya ce masu hada maganin tari su rinka amfani da Dextromethorphan wanda bai kai kodin illa ba.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here