Hakan ya biyo bayan matakin ne sakamakon wani harin kunar bakin wake da bam-bamai da aka kai wani masallaci da ke kasuwar garin Mubi wanda ya kashe akalla mutum 27 tare da jikkata wasu da dama.
Mataimakin shugaban kasar Farfesa Yemi Osinbajo wanda ya bada umurni ya kuma umurci hukumar agajin gaggawa ta kasa wato NEMA ta gaggauta samar da magunguna da sauran kayayyakin agaji ga wadanda lamarin ya rutsa da su.