YADDA AKA KIFAR DA GWAMNATIN BUHARI A 1985 Kashi na uku

0

YADDA A KIFAR.GWAMNATIN BUHARI A 1985.. Kashi na uku..

Fitowa ta uku

A na saura kwana daya  sallah Babangida ya bar Legas ya tafi Minna
hutun sallah, bayan duk sun gama yin tsare-tsarensu na juyin mulkin.
A ranar 26 ga watan Agusta 1985, ita ce ranar da Musulmi ke bikin
Babbar sallah a fadin kasar, a kuma wannan ranar ce wadanda suka
shirya juyin mulkin, suk tsara aiwatar da shi da marecen ranar. Shi
yasa tun safe suka kasance cikin shirye-shirye na tabbatar da juyin
mulkin, musamman a babban birnin tarayya na Legas.

Kafin Babangida ya bar Legas sai da ya nada  Manjo Abdulmumini Aminu a
matsayin wanda zai jagoranci juyin Mulkin a Legas. Ina da kware Ikeja
a matsayin cibiyar juyin mulkin, sannan sun tanadi motacin rokokin na
fada sun ajiye su gefe guda koda taka je ta dawo.
Littafin ya rawaito cewa, kusoshin da suka shirya juyin mulkin, sun
zabi babban dakin taro na Bonny Camp da kuma wasu gidajen shakatawa a
Victoria Island a Legas, domin su shirya duk wasu tsre-tsare da suke
bukata.

A wannan ranar ne Shugaba Buhari ya fahimci cewa akwai wani abu marasa
kyau da ke shirin faruwa, sai ya umurci, Kwamanadan da ke  tsaron
gidan gwamnati  Lutanal Sabo Aliyu da ya binciko abin da ke shirin
faruwa, wannan yasa Sabo Aliyu ya tambayi abokin aikinsa  Lutanal
Koloniyan  Halliru Akilu, wanda shi ne daraktan hukumar kula da tsaro
da kasa, sai Halliru Hakilu ya nuna mashi bai san wani abu ba, kan
wannan abun kuma ba gaskiya ba ne, sai dai abin da  Sabo Aliyu bai
sani ba Halliru Hakilu ya na da ga cikin wadanda ke tsara juyin
mulkin.

Baki daya Koloniyal Sabo Aliyu hankalinsa bai kwanta kan yadda abubuwa
ke faruwa ba, sam hankalinsa bai kwanta ba saboda ya na ta ganin alamu
da ke nuna yiwuwar wannan jita-jita ta juyin mulki. Wannan yasa
Koloniyal Sabo Aliyu da Dogarin Buhari Manjo Mustapha Jokolo, suka yi
tattaki zuwa Ikoyi da Victoria Island domin samun wasu labarai ko kuma
samun wani karin haske kan wannan abu da ke jita-jita kansa, amma basu
samo wani labari ba wanda zai tabbatar masu da wani abu kan
jita-jitar.

Wannan rana ta Sallah Buhari bai samu kwanciyar Hankali ba saboda
abubuwan da ya ga suna faruwa, sai ya xauki waya ya kira Birgediya
Sani Abacha, a matsayinsa na shugabn bayar da tsaro a Legas baki daya,
amma yai ta kiransa bai same shi ba, ya sa aka tura Signal ga
Birgediya Sani Abacha, amma duk ba a same shi ba, hankalin Buhari ya
tashi sosai kan rashin samun Birgediya Sani Abacha, wannan ya sa mai
kula da tsaro na fadar Shugaban kasa  Sabo Aliyu ya tura Kaftin
Maitama  zuwa Ibadan domin ya je ya sanar da Abacha halin da ake ciki,
Kaftin Maitama ya je ya dawo ba tare da ya ga Abacha ba, sai da abin
da Buhari da Sabo Aliyu ba su sani ba shima Maitama ya na daga cikin
wadanda suka shirya juyin mulkin.

Bayan Buhari ya ga za samun Abacha sai ya yank hukuncin ya nemi
Babbangida domin ya sanar da shi halin da ake ciki, musamman ma saboda
shi ke kula da duk wasu tankokin yaki da manyan makamai. Buhari ya
kira Babangida ya fi a kirga amma ba a dauki wayar ba, amma cikin
sauki kuma Abdulmumini Aminu ya ke kiran Babbangida ya na samun shi,
amma ga shugaban kasa ya kira an ki a daga. Wannan abu ya sanya Buhari
shiga cikin matsanaciyar damuwa.

Da marece ranar sallar  Laftanar Kanal Sabo Aliyu da Dogarin Shugaban
Kasa, Mustapha Jakolo, suka dauki mota daga fadar shugaban kasa suka
tafi Ikeja domin samo bayanai kan abubuwan da ke faruwa, tun a bakin
kofar shiga a ka tsaresu karkashin shugabancin Manjo John Y. Madaki da
Manjo Maxwell Khobe, inda suka sa aka tasar keyarsu har a gidajen
manyan Sojoji na barikin  Bonny Camp.

Gabaki daya hankalin Buhari ya tashi a fadar Shugaban kasa ta Dodon
barek, ga shi dai shiru Dogarin sa da Sabo Aliyu basu dawo ba, kuma
bai san halin da suke ciki ba, sannan kuma Mataimakinsa Idiagbo ya na
Saudiyya, sannan ya kira Babbangida yaki samunsa a waya, haka ma wanda
ke kula da tsaro a Legas Abacha shi ma an ki samunsa.

A wannan lokaci mutanen da suka ragewa Buhari kusa duk basu da wani
karfi na makamai da zasu iya tsayar da wani yunkuri da ya shafi juyin
mulki, domin daga Lawal Rafindadi, sai Dumkan Bali sai Manjo Janar
Muhammada Mangoro minisata harkokin cikin gida. Buhari bai da tabbas
da Dumkan Bali, shi kuma Mangoro wadanda ke karkashinsa kwastam ne da
jami’an gidan yari wadanda su kuma basu da karfin da zasu iya tsaida
juyin mulki.

Sauran wadanda ke tare da shi dari bisa dari sun hada da Manjo Janar
M.D Jega, wanda shi kuma a lokacin ya yi nisa domin yana Adamawa, sai
kuma Birgediya Salihu Ibrahim, wanda shi kuma a lokacin ya na Jos.
Wannan yasa dole Buhari ya nemo wasu sojoji da zasu bashi tsaro a
fadar shugabn kasa, sai dai cikin rashin sani wadannan sojojin da ya
kawo duk sun daga cikin wadanda aka tsara juyin mulkin da su.
Da karfe tara na dare a ranar 26 ga wata Augustan 1985 wasu hafsoshin
soji hudu suka kutso kai cikin fadar shugaban kasa, wadannan hafsoshin
sojin sun hada da;
•       Manjo Abubakar Dangiwa Umar
•       Lawal Gwadabe
•       Abdulmumini Amini
•       Sambo Dasuki
Wadanna sojiji suka tsare Buhari da bindiga suka tasa keyarsa gaba har
barikin Bonny Camp inda aka tsare Dogarinsa da kuma Sabo Aliyu suka
hada su a cen , sannna daga baya suka wuce da su zuwa Benin kamar
yadda aka hakalto a cikin littafin.

Sauran sojijin kuma duk su tare hayoyin da za aiya fita ko kuma shiga
Legas, sojojin da ke tsaron gidan Buhari kuma duk suka dauke wasu
abubuwa wadanda suke mallakin Buhari ne a gidan. Duk wadannan abubuwan
da ke faruwa Babangida ya na Minna hutun sallah tare da iyalinsa.
Ranar 27 ga watan Agusta da karfe goma na safe, sojojin da suka shirya
juyin mulkin suka sanar da duk wani bariki na soja abin da ake ciki
domin daukar matakin da  ya dace. Sannan duk wasu kusoshin da suka
shirya juyin mulkin suka nufi Legas a ranar, sanarwa ta samu Babangida
na an yi kome cikin nasara, wannan ya sa Babangida ya hawo jirgi ya
nufo Legas domin ya karbi shugabanci kamar yadda a ka tsara. Duk wa su
kusoshin da suka shirya juyin mulkin wadanda suka hada da  Koloniyal
Aliyu Gusau  sun hadu sun yi taro inda Birgediya Sani Abacha ya sanar
da cewa, Ibrahim Babbangida sh ne Shugaban kasar Nijeriya a yanzu.
Da Marece Babbangida ya fito a gidan Tallabijin na NTA ya yiwa ‘yan
kasa jawabi, a matsayinsa na Shugaban kasar Nijeriya, tare da shi
akwai,  Joshua Dogonyaro, da Halliru Akilu da kuma John Shagaya.
Wanna shi ya kawo karshen gwamnatin Buhari kamar yadda aka hakalto a
cikin littafin.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here