Jarumar Finafinan Hausa Hauwa Maina Ta Rasu

0
627

Shahararriyar jarumar nan ta fina-finan Hausa Hajiya Hauwa Maina ta rasu jiya Laraba da daddare.

Rahotanni sun bayyana cewa ta rasu ne a asibitin Malam Aminu Kano bayan ta sha fama da jinya.

Ana sa ran za a yi jana’izarta a  yau Alhamis a garin Kaduna, inda take zaune gabanin rasuwarta.

Hauwa Maina na daga cikin matan da suka jima suna fitowa a fina-finan Hausa.

Tun 1999 ta fara fim din Hausa, bayan ta koma garin Kaduna da zama.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here