KASASHE GOMA DA SUKA SHAHARA WAJEN CIN ZARAFIN MATA DA YI MASU FYADE

0

KASASHE GOMA DA SUKA SHAHARA WAJEN CIN ZARAFIN MATA DA YI MASU FYADE

Daga Abdurahaman  Aliyu

Keta hakkin mata da muzantasu ya zama ruwan dare a wannan zamani da
muke ciki, kusan kullum sai ka samu labarin matan da aka yi fyade ko
kuma aka ci mutuncinsu ko tozarta su a rayuwa. wannna abu ya shahara
kuma ya yi kamari a kasashe da dama, musamman kasashe masu tasowa.

Mujallar Wanderslist  ta yi wani nazari in da ta fito da kasashe guda
goma wadanda aka fi cin zarafin mata a duniya, kuma wani abun mamaki
da yawa daga cikin kasashen, kasashe ne da suka cigaba kuma suka
shahara a duniya, ga jerin kasashen kamar yadda mujallar ta wassafo
su;

10.Ethopia  it ace masa ta goma da aka fi samun rigingimu da muzanta
mata a duniya, kusan kasha sittin cikin dari  (60%) na matan da ke
Ethopia an keta haddinsu ta fuskar cin zarafi, ko dai fyade ko kuma yi
masu aure da kanana shekaru, Ethopia ta yi kaurin suna wajen garkuwa
da yara mata, tare da yi masu fyade, wani lokaci har ciki ya shiga.

9. Sri Lanka: kasa ce da ke fama da matsalar cin zarafin mata ta
fuskar fyade. Kasa ce da ta sha fama da yakin basasa, wanda bayan kare
yakin aka samu korafe-korafe da daman a yiwa mata fyade a kasar,  kusan
14.5%  na mazan Sri Lanka sun taba yin fyade a rayuwarsu, kashi 4.9%
sun yi fyade a baya, kasha 95.9% kuma suna tare da kungiyoyin yiwa
mata ko kanan yara fyade, sannan kashi 65% ba a cika hukunta su ba
saboda wasu dalilai, wannan ne yasa kasar ta kasance mafi rinjayen
kasar da mata ke kunar bakin wake a duniya baki daya.

8.Canada; kasa ce da ke yankin Amurka kasa ce da aka samu koken fyade
miliyan biyu da dubu dari biyar da sha shidd da dari tara da sha
takwas (2,516.918) wannan kashi shidda ne kacal cikin dari da aka
kaiwa jami’an ‘Yansanda rahoto. Kamar  yadda wata cibiya mai suna Justice
Institute of British Colombia ta rawaito, ta ce a Canada duk cikin
mace goma sha bakwai (17) sai an samu wadda aka taba yiwa fyade.

7.France: fyade bai zama laifi ba a Faransa sai a shekara 1980, lokacin
da aka kirkiri dokar kare yancin mata da samar masu da natsawu.
Faransa ita ce kasa ta bakwai  wajen keta hakkin mata da yi masu fyade
in da take da rahoton yi wa mata fede sama da miliyan uku da dubu dari
bakwai da saba’in da daya da dari takwas da hamsin (3,771,850).

6.Germany: sama da mata dubu dari biyu da arba’in suka mutu a Germany
sakamakon keta haddinsu ko kuma yi masu fyade. Germany ta zama kasa ta
shidda ne saboda samun rahoton yi wa mata miliyan shidda da dubu dari
biyar da bakwai da dari uku da tisi’in da hudu a wanann shekarar.

7.United Kingdom: mutane da yawa suna mafarkin su ziyarci UK, saboda
kasancewarta kasar da ta shahara a duniya a bangaren cigaba, amma kuma
a gefe guda kasa ce da ta shahar bangaren yiwa mata fyade da keta
haddinsu.

A shekarar 2013 ne mai’aikatar Shari’a ta kasar ta fitar da
wani jaddawali kan cin zarafin mata da yi masu fyade, wannan
jaddawalin ya nuna cewa, duk shekara ana yiwa mata sama da dubu
tamanin da biyar fyade a Ingila da kuma Wales. Fiye da mata dubu dari
hudu ne ake muzantawa da cin zarafinsu a ko wace shekara. Mujallar ta
bayyana cewa mace wadda ta kama daga shekara 16-59 to tana damasaniya
kan wani abu day a shafi cin zarafin mata.

4. India: kasar Indiya kasa ce da kullum cin zarafin mata yake karuwa
madadin raguwa, fyade a Indiya shi ne laifin da ya zama ruwan dare
wanda ba a dauke shi bakin kome ba. Kamar yadda hukumar kula da manyan
laifuka ta kasar ta sanar a 2012 an kawo rahoto fyade sama da 24,923.
Amma kwararrun masu bincike sun tabbatar dacewa wannan rahoto zuki ta
malle ne kawa, domin wadanda ake yiwa fyade a Indiya sun haura wannan
adadin, domin sun bayyana cewa duk cikin minti ashirin da biyu a
Indiya sai an samu rahoton fyade.

3.Sweden: Sweden na daya daga cikin kasashen da suka yi kaurin suna
wajen yiwa mata fyade in da bincike ya bayyana cewa duk cikin mata
hudu sai an samu wadda aka taba yiwa fyade a Sweden. Kuma wani abun
ban haushi duk shekara sai an kara samu hauhawar adadin matan da ake
yiwa fyade a kasar.

2.South Afrika: Wannan kasar ita ce ta biyu wajen korafe-korafen cin
zarafin mata da keta haddin su a Duniya, sanna wannan kasar ita ce
kasar da tafi kowace kasa yawan yi wa kananan yara fyade. Rahoton
yabayyana cewa mace uku cikin huda an taba yi masu fyade ko kuma an
taba cin zarafinsu a matsayinsu na mata.

1. United State: kasa mafi shahara a Duniya, kuma kasa mafi shahara
wajen yiwa mata fyade a duniya. A US kusan kasha 91% na waxanda ake
yiwa fyade mata  ne, sannan kasha 99% na masu yin fyaden maza ne,
kamar yadda hukumar kula da hakin mata ta kasar ta rawaito, ta
tabbatar da cewa mace daya cikin shidda a US tana da wata masaniya kan
fyade ko an taba yi mata fyade, sannan namiji daya cikin 33 a US ya
taba yin fyade ko ya jaraba yin fyade. Sannan an sha samun koken yiwa
mata fyade ko kuma jaraba cin zarafinsu tun suna shekara sha hudu a
Duniya.

Daga Abdurahaman  Aliyu

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here