Kotu Ta Ba ‘Yansanda Umurnin A Garkame Sanata Dino Malaye

0

Wata kotun majistire a jihar Kogi ta ba ‘yan sanda umurnin a garkame Sanata Dino Melaye har zuwa ranar 11 ga watan Yuni don cigaba  da tuhumar da ake yi masa.

An gurfanar da sanatan mai wakiltar jihar Kogi ta yamma a gaban babbar kotun majistire ne kan laifuka bakwai da ake tuhumarsa da suka hada da mallakar makamai.

A yayin sauraran qarar, an shigar da sanatan cikin kotun ne kan abin daukar marasa lafiya.

Sai dai Sanatan ya musanta dukkanin zargin da ake ma sa, wadanda ya ce siyasa ce kawai.

Lauyan da ke jagorantar lauyoyin da ke kare shi, Mike Ozekhome ya nemi babban alkalin majistire, Suleiman Abdullahi, ya bayar da belin Melaye domin yana da cutar asma da ke bukatar kulawa.

Sai dai kuma lauyan da ke gabatar da kara Alex Iziyon, ya bukaci kotun ta garkame sanatan da wadanda ake tuhuma tare da shi domin ‘yan sanda su samu damar ci gaba da bincikensu.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here