Sabon Hari: An Kashe Mutum 43 A Kauyukan Adamawa Da Zamfara

0

Rahotanni na bayyana cewa, akalla mutum 43 aka kashe a wani sabon hari da wasu ‘yan bindiga suka kai kauyukan jihar Adamawa da Zamfara. 

An daikai harin kauyaku uku da ke karamar hukumar Numan ta jihar Adamawa inda aka kashe mutum 30 wasu da dama suka bace ba’a san inda suke ba a garin.

A Zamfara kuwa an samu rahoton kashe akalla mutum 13 a kauyen Fankashi dake karamar hukumar Maru a jihar, bayan wata arangama da aka yi tsakanin ‘yan banga da wasu mahara da suka afkawa garin.

Shugaban karamar Hukumar Numan Arnold Jibila, ya tabbatar da aukuwar wannan harin a kauyukan, mazauna garin sun bayyanawa manema labarai cewa, maharan sun shiga kauyuku shida na karamar hukumar da suka hada da: Bolki, Bang da kuma Gon da misalin karfe bakwai na daren ranar Alhamis sun kone gidaje da dama tare da yin harbe-harbe a garin.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here