Abubuwa goma da ya Kamata ka Sani Game da Kungiyar ISIS

0

*Abubuwa goma da ya Kamata ka Sani Game da Kungiyar ISIS*

Daga Abdulrahman Aliyu

An kirkiri Kungiyar Islamic State in Iraq anda Syria (ISIS)a shekarar
1999 a karkashin jagorancin Abu bakr al-Baghdadi, amma Abu Musab al-Zirqawi ne ya
kafa ta  da sunan Jama’at  al-Tawhid wal-Jihad, ta hade da kungiya
Al’Qa’ida a watan Octoba shekarar 2004. Ta sauya suna zuwa Islamic
State a ranar 13 ga watan Oktoba 2006. Ta ayyana kanta matsayin mai
jin gashin kanta a ranar 8 ga watan Afirilun 2013, ta baranta kanta da
kungiyar Al-Qa’ida a ranar 3 ga watan Fabarairun 2014.

Ta kaddamar da
shugabaninta a ranar 29 ga watan Yuni a shekarar 2014, sanna ta yi
ikirarin cewa ta na da manyan rassa a Libiya da Egypt da Algeria da
Saudi Arebia da Yemen  a ranar 13 ga watan Nuwamba 2014.

Ta kaddamar
da reshenta na Kudancin Asiya a ranar 29 ga watan Janairun 2015.
Sannan ta kaddamar da reshenta a Nijeriya a ranar a ranar 12 Mach
2015.

Daya daga cikin Wakilan Taskar Labarai Abdurrahman Aliyu ya binciko
mana wasu abubuwa goma da ya kamata ace kowa ya sani game da wannan
kungiyar.

1.      Matsayin Kalmar ISIS:  kamar yadda sauran Kungiyoyin masu amfani da wasu
kalmomi a matsayin inkiya ko kuma gajarta sunan su, irin su USA da WHO
da sauransu, kungiyar ISIS ita ma tana amfanin da wadannan kalmomin a
matsayin sunanta a yankunan Iraq da Syria. Yayin da ta ke amsa sunan
ISIL a bangaren Iraq da Levent.

2.       Manufar Kungiyar ISIS: manufar wannan kungiya shi ne kafa Kasar
Musulinci da dawo da Jagoranci irin na musulunci, da kuma dawo da
musulunci a yankin, kamar suke ayyanawa.

3.      Rayukan da ISIS ta Salwantar da Sunan Jihadi: wannan kungiya ta kashe
mutane sama da 1400 a jihohi 21 da ta ke da iko, sannan ISIS sun kai
hare-hare a kalla guda 90 a duk fadin Duniya.

4.      Hanyoyin Samun Kudin Shiga na ISIS : a kwai mamaki kan yadda
kungiyar ta ke samun kundin shiga, amma a zahiri in an yi la’akari da
ayyukan kungiyar ba abin mamaki ba ne, domin ana zaton suna da wani
shiri da kasar Turkey da suke samun mai. Sauran hanyoyin sun hada da;
Garkuwa da mutane da sumogal daSata da saiyarda wasu kaya da suka
kwace da sauransu.

See also  MACE MAI TUKA KEKE NAPEP A KANO

5.      Yadda suke Daukar Ma’aikata: Kungiya ISIS su na da hanyoyin da suke
daukar ma’yakansu da masu yi masu aikace-aikace, musamman saboda kudin
da suke biya. Ana samun mutane da yawa daga fadin Duniya suna tafowa
domin shiga wannan Kungiya. A kalla mutane dari shiddda (600) sun tafo
daga UK sai kuma wasu kusan 400 daga US da Canada domin su hada hannu
da wannan kungiyar.

6.       Rusa  kayan Tarihi da na Bauta: wannan kungiya ta kure wajen rusa
wasu kayyakin tarihi musamman na addinai da sauran makamantansu a
kasashen da suke da iko, sau da yawa kayan da suke rusawa suna tafiya
da wasu ne sai su sayar da su domin samun kudaden shiga na gudanar da
kungiyarsu.

7.      Cinikin Bayi: Kungiya ISIS ta na da mutanen da ta ke kira bayi musamman
mata da kanan yara wadanda take kamowa a yayin hare-haren da kungiyar
ta kai,  duk cewa  an hana cinikin bayi a yanzu, amma wannan kungiya,
har yau ta na sayar da bayi domin samun kudin shiga.

8.      Karfin ISIS; wannan kungiya na da karfin da ta ke tsaye da kanta,
domin har kudi suna bugawa na kashin kansu, sannan su na da wuraren da
suka amshe daga hannun gwamnati suna kula da shi da kansu, wato
karkashin ikonsu ya ke. Sannan duk wani abu da suka sayar suna bada
rasidi  mai dauke da sunan ISIS, haka ma duk wasu takardu da za su
fito daga wurinsu suna dauke da sunan ISIS

9.      Matsayin Ilimin Mayakan ISIS: mafi yawan kungiyoyin jihadi na Musulunci da
ake samu suna fitowa ne daga kasashe masu ilimin addaini, sannan ana
samun masu tsatsauran ra’ayin addini a cikin su, su ne kre jagoranta
ayyukan jihadi na tayar da kayar baya. Amma abun mamaki a ISIS ba haka
abin ya ke ba, mafi yawan mayakan sun fito ne daga kasashen USA da
Canada da wani yanki na Yammacin Turai, su ne ke shiga wannan kungiya
ta ISIS. Sannan suna da ilimin zamani wanda ya hada da Injiniyoyi da
Likitoci da Akawu da kwararru waj

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here