Gwamnan Jihar Kaduna Nasir Ahmad El-Rufai a jiya Litinin ya ziyarci garin Gwaska da ke qaramar Hukumar Birnin Gwari inda wasu’yan bindiga suka afkawa mazauna tare da kashe wasu da dama a ranar asabar.
A yayin ziyarar Gwamnan da ya kai garin Birni Gwari da misalign karfe 12 na rana, ya kuma ziyarci masarautar garin inda ya gana da Sarkin Birnin Gwari, Malam Jibril Zubair II, a fadarsa tare da wasu hakiman garin.
Sarkin ya bayyana wa Gwamnan cewa, masarautar ta samu rahoton cewa su nada adadin mutane 58 da aka kashe a yanzu kuwa adadin ya karu zuwa mutane 13, yayin da kuma gwamnatin jihar ta samu rahoton kisan mutane 45 kamar yadda kwamishinan ‘yan sandan jihar Austin Iwar ya sanar a ranar Lahadin da ta gabata.