Allah Ya Yi Wa Khalifa Isyaka Rabi’u Rasuwa

0

Allah ya yi wa Shugaban Darikar Tijjaniya a Najeriya Khalifa Isyaka Rabi’u, rasuwsa.

Daya daga cikin ‘ya’yan marigayin ya shaida wa manema labarai cewa ya rasu ne a wani asibiti a birnin Landan na Ingila a yammacin ranar Talata.

Marigayin, wanda ya sha fama da rashin lafiya a ‘yan kwanakin nan, ya rasu ne yana da shekara 90 a duniya.

Baya ga malantaka, marigayin kuma hamshakin dan kasuwa ne wanda ya yi fice a fagen kasuwanci a Najeriya.

Bayanai sun za a yi janazar marigayin da zarar gawarsa ta iso Najeriya daga birnin Landan, inda ya rasu.

Ya rasu ya bar mata hudu da ‘ya’ya 42 da kuma jikoki da dama cikinsu har da Alhaji Abdussamad Isyaka Rab’iu, wanda shi ne shugaban hadakar kamfanin BUA.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here