AN GUDANAR DA TARON SAMARWA MATASAN JIHAR KATSINA MAFITA A SHIYYAR DAURA

0

AN GUDANAR DA TARON SAMARWA MATASAN JIHAR KATSINA MAFITA A SHIYYAR DAURA.

Daga

Bishir Suleiman

Kammafinin ɓunƙasa zaman lafiya da tsaro ( Peace Builders Security Concepts) da haɗin guiwar gwamnatin jahar Katsina sun gudanar da taron bita kan lamuran sha da fatacin miyagun ƙwayoyi a tsakanin matasa, taron ya gudana, a ɗakin taro na Muhammad Buhari da ke Daura Motel.

Taron ya samu halartar Sakataren gwamnatin jahar, Alh. Dakta Mustapha Muhammada Inuwa wadda shi ne babban mai gabatarwa kuma wakilin mai girma gwamnan jahar Katsina, Alh. Aminu Bello Masari, haka kuma taron ya haɗa masu ruwa da saki a jahar nan, kama daga iyayen ƙasa da Malaman addini da kuma masana daban daban daga jami’o’i da manyan makarantu.

Da yake jawabin a wurin taron shugaban kamfanin Alh. Wada Maida ya nuna farin cikinsa ga yadda masu ruwa da tsaki suka halarci taron domin a samu hanyar da za a fitar da a’i daga cikin duma kan lamuran shaye shaye a tsakanin matasa.

Kazalika, ferfesa Muhammad Ali Garba Malumfashi a takardar da ya gabatar mai taken: Samar da kafar gina makomar matasa, ta hanyar inganta rayuwarsu a jahar Katsina, takardar ta yi bayanin kan yadda yara basa sa samun shiga makaranta da yadda ake samun matsalar faɗuwa jarabawar share fagen shiga manyan makarantu da kuma yadda ƙalilan ne ke samun nasara samun takardun shiga manyan makarantun.

Haka kuma, takarda ta zaƙullo shirye shirye da dama da ake gudanarwa kan matasa, amma har yanzu da sauran rina a kaba domin ba waɗanda suka dace bane ake baiwa tallafin dogaro da kai ba, daga ƙarshe ya yi tsokaci mai dama kan yadda za a magance matsalar a tsakanin matasa.

Da ya ke nasa jawabin Sakataren gwamnatin jahar Katsina, Dakta Mustapha Inuwa ya yaba ƙwarai da ƙoƙarin kamfanin bisa ga dogon tunani da ya yi kan samarwa matasa mafita, ya kuma bayyana tsare tsaren gwamnatin Masari kan bunƙasa matasa, kamar shirin Spower da aka kirkiro dan samar da aikin malanta da shirin koyar da sana’o’i, dama na bunƙasa harkar noma duk dan a tallafi rayuwar matasa.

See also  WASIKA GA GWAMNAN KANO AKAN MASARAUTAR KANO

Kazalika, Shugaban gudanarwar kamfanin mai rajin bunƙasa zaman lafiya da tsaro Alh. Ibrahim Katsina ya yi godiya ga gwamnatin jahar katsina bisa ga yadda suka maida hankali wajen ceto rayuwar matasa da yadda suke haɗin guiwa da kamfanoni da masu ruwa da tsaki kan yaƙar wannan mumunar ɗabi’a a tsakanin matasa.

A takardar da ta gabatar dakta Alder Ade mai taken mahimmacin kafa cibiyar kula da masu shaye shaye, ta bayyana mamakinta kan yadda ake tafiyar da rayuwar mashaya a ƙasar nan, ta hanyar kama su da ƙyamatar su a cikin al’umma, maimaikon a lura da cewa su fa marasa lafiya ne, suna buƙatar a kula da lafiyar su maimakon a rinƙa kama su ana ɗaurewa.

Ta ƙara da cewa, in aka kula da lafiyarsu ta hanyar yi masu jinya, itace kaɗai hanyar da za a magance lalurar ta su.

Da ta ke tofa albarkacin bakin ta shugabar kwalejin shari’ah da sauran kwasa kwasai ta Daura a jahar Katsina, ferfersa Sa’adiyya Sani ta yi nuni da cewa ɓacin rai da tashin hankali da shiga ƙungiyoyin da basu dace ba ke haifar da yawaitar shaye a tsakani matasa, dan haka sai al’ummah, ta tashi tsaye kan wannan yaƙi, dan yaƙi ne da ya shafi kowa da kowa.

A jawabin Mai martaba Sarkin Daura ta bakin Turakin Daura Alh. Musa Musa Abdulrahman ya yi godiya ga gwamnatin jaha da kamafanin da suka assasa taron, da dukkan mahalarta taron bisa ga girmamasu da aka yi aka kawo taron Shiyar Daura, ya ƙara da cewa mai martaba na namijin ƙoƙari kan sanya matasa hanyar da za inganta rayuwarsu da kuma wayar da kansu kan illar shaye shaye.

Bishir Suleiman
Jaridar Taskar Labarai

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here