Bakatsine Ya Daukaka sunan Nijeriya a Idon Duniya

0

Bakatsine Ya Daukaka sunan Nijeriya a Idon Duniya

Daga Abdurrahaman Aliyu

Abdulmumini Sani Mati dan kimanin Shekaru 20 haifaffen dan Jihar Katsina da ke karatun digiri na farko a sashen Kudi da kididdiga a Jami’ar City da ke Kasar United Arab Emirates ya kafa tarihin tare da daukaka sunan Nijeriya a Idon Duniya, a wata gasa da aka yi a United Arab Emirates, kan Kudi da kididdiga da kuma tattalin arziki.

Ministan Illimi na United Arab Emirates Ibrahim Al- Hammadi ne ke shirya gasar ga daliban da ke karatun digiri na farko a Jami’ar Abu Dhabi.

Abdulmumini Sani Mati ya shiga wannan gasa da aikin sa mai taken: “Kididdiga bisa tsarin Mazan jiya: wasu Hanyoyin Samun Nasara”. In da ya zo matsayin na biyu cikin dalibai dari tara (900) da suka shiga gasar daga jami’o’i arba’in (40) a fadin Daular Larabawa.

See also  FG Inaugurates Road, Gully Erosion Intervention Project At UNIBEN

Abdulmumini Sani Mati ya gabatar da takardar ne da taimakon malaminsa Dalta Faisal Khan mataimakin Farfesa a sashen Nazarin Kudi da kididdiga na Jami’ar City.
Shugaban Jami’ar City Mr Imran Khan da mataimakin Shugaban Jami’ar  Dr Mohammad Amerah  sun Taya Abdulmumini Sani Mati murnar nasarar da ya samu da kuma daga martabar Jami’arsu da ya yi.

Abdulmumini Sani Mati shi ne na farko da ya taba samun wannan matsayi a duk fadin Afrika ba ki daya.

Muna taya Abdulmumini Sani Mati murna wannan nasara da ya samu ta daukaka darajar Nijeriya, muna alfahari da shi kuma masa fatan Alheri da samun Nasara.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here