An cafke ƙasurgumin ɗanta’adatar da ya shahara wajen garkuwa da mutane

0

An cafke ƙasurgumin ɗanta’adatar da ya shahara wajen garkuwa da mutane

Shugaban ƴanta’adatar da ya shahara wajen kashe mutane da yin garkuwa da su, wadda ake kira da Barau Ibrahim aka Rambo, sun gwanace wajen yin ta’adanci a yankunan Birnin Gwari da ke a jahar Kaduna, da hanyar Abuja, Kaduna da Kano da kuma Jahar Zamfara, an damƙe shi ne ɗauke da manyan Bindigu kirar AK 47 guda biyu shakire da harsasai guda hamsin da ɗaya.

An damke jagoran ƴan’ta’adatar ne a ranar 13/5/2018 wajajan karfe ɗaya da rabi na dare. Wanda rundunar ƙwararru masu jiran ko ta kwana IRT tare da haɗin guiwar rundunar ofiration natsuwa wadda Shugaban rundunar ƴansanda ta ƙasa Alh. Ibrahim K Idris ya kafa sun damke ƙasurgumin ɗanfashi dake kashe mutane da yin garkuwa da su, wanda ake nema ruwa a jallo, ya kuma addabi yankin Marabar Yakawada dake a ƙaramar hukumar Giwa a jahar Kaduna, Bara’u Ibrahim aka Rambo ya shahara wajen aikata laifuka wanda ya ke aika aikarsa ta hanyar amfani da bindigogi guda biyu kirar AK 47 a lokaci guda.

See also  ???????? ??????? 450: ?????????, ??? ????? ?? ???? ??? ???!

Haka kuma, rundunar ta yi nasarar kame wani daga cikin ƴanrudunar da ake kira Shehu Abdullahi aka Gashin Baki mai shekaru 40 rundunar ta damke shi ɗauke da bindigu biyu kirar AK 47 masu ɗauke da lamba: Ad160102 da kuma 1978AD4328 da kuma harsasai guda hamsin da ɗaya (51) haka kuma a ofirashin ɗin an samu Rambo da ƙaramar mota kirar gob (VW Golf)

Rundunar IRT ta sha alwashin kawar da dukkan ƴan’ta’adda da suka addabi jahar da kashe kashen jama’ah da yin garkuwa da su.

Bishir Suleiman Jaridar Taskar labarai

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here