ANA YIMA OFISHIN SAKATAREN GWAMNATIN KATSINA GYARAN FUSKA

0

ANA YIMA OFISHIN SAKATAREN GWAMNATIN KATSINA GYARAN FUSKA

Daga Wakilanmu.

Wani aiki da Jaridar Taskar Labarai ta tabbatar yana gudana yanzu haka a ofishin sakataren gwamnatin jihar Katsina Dakta Mustafa Muhammad Inuwa, shi ne wani gagarumin gyaran fuska da ake yi Wanda ba a taba kamar sa ba tunda aka gina sakatariyar.

Aikin kamar yadda binciken mu ya tabbatar ya shafi iyar ofishin na sakataren gwamnati kawai, In da yake zama, bai kumshi sauran ofisoshin ba.

Wajen da aikin ya kunsa ya hada da Inda yake zama da wajen zaman jiran bakin da suka zo ganin sakataren da ofishin P. A na shi da dakin taron dake hade da ofishinsa da kuma ofishin nasa.

Aikin Wanda jaridar ta gano ana yinshi cikin sirri, kuma har wasu lokutta da dare ana aiwatarwa kamar yadda wata majiya ta tabbatar wa da jaridar, majiyar ta ce, “har wani lokaci da yamma da kuma dare aikin na gudana”

Wannan yasa ma’aikatan ofishin sakataren suka koma ofishin babban sakataren sasahen wanda daga can suke gudanar da aikin su, na amsar takardun da aka kawo wa sakataren.

Wannan aiki da akeyi a sirrance kuma a tsanake ya dau kwanaki har ya zuwa rubuta labarin nan ba a kammala shi ba.
A farkon hawan gwamnatin APC Bayan nada Dakta Mustafa Muhammad Inuwa sakataren gwamnati, daya daga cikin ayyukan da yayi shi ne, gyaran fuska da canza fasalin ofis dinsa dake cikin gidan gwamnatin Katsina. Wanda ke harabar rukunin ofisoshin, dake tattare da na gwamnan Katsina.

A farkon tsarin wajen ofis biyu ne a jere daya sakataren gidan gwamnatin Katsina Muntari Ibrahim na amfani da shi, dayan kuma Furotokol na gwamna Rabiu Idris na amfani da shi.

Zuwan gwamnatin APC sai sakataren gwamnati ya sanya aka yi sabon aiki aka canza fasalin aka kuma hade masa su,
Shi ma aikin na canza fasalin ofishin an yi shi ne kamar yadda ake yin na ofishin sakatariyar jahar.

Daya daga cikin marubutan Jaridar ya tuntubi jami’in hudda da jama’a, na ofishin sakataren gwamnatin.a kan wannan aiki, jami’in Alhaji Abdullahi Aliyu Yar’adua, yace, ba abin da zai ce a kan wannan aikin.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here