AN KASHE MANAJAN KAMFANIN DANGOTE

0

AN KASHE MANAJAN KAMFANIN DANGOTE

Majiyar BBC Hausa ta rawaito cewa,
An kashe manaja da ma’aikata biyu na kamfanin simintin attajirin da ya fi kowa kudi a Afirka, Aliko Dangote, a yankin Oromia na kasar Habasha.

Manajan wanda dan kasar Indiya ne mai suna Deep Kamara ya mutu ne tare da wadansu ‘yan kasar Habasha biyu.
Wata sanarwa ta ce suna kan hanyarsu ta dawowa daga babban birnin kasar, Addis Ababa, ne a lokacin da lamarin ya faru.
Akwai rahotannin da ke cewa Dangote zai kai ziyara kasar a ranar Alhamis.
Jaridar Addis Standard ta Habasha ta bayar da rahoton cewar attajirin zai yi ganawar gaggawa da shugabannin masana’antar hada simintin.

Yankin Oromia ya shafe shekara biyu yana fama da tashe-tashen hankali masu nasaba da matsin tattalin arziki da siyasa daga matasan Oromo- wadanda su ne suka fi yawa a kasar.
An kafa kamfanin simintin Dangote ne a watan Mayun shekarar 2015 kuma masana’antar ce mafi girma a kasar.
Kwanan nan ne aka tilasta wa hukumomin kasar su soke sabunta lasisin mahakar zinari na wani biloniya wanda dan Habasha da Saudiyya ne bayan zanga-zangar mazauna Oromia.
Yanzu dai kasar tana cikin dokar ta-baci ne, wadda aka ayyana a watan Fabrairu wato rana daya bayan Farai ministan Hailemariam Desalegn, ya yi murabus.
Abiy Ahmed ne ya maye gurbinsa a matsayin firai minista daga kabilar Oromo, wadda ta fi rinjaye.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here