Sakamakon Zaben Kaduna: APC Ta Samu 14 PDP 4

0

Sakamakon Zaben Kaduna: APC Ta Samu 14 PDP  4

Hukumar zaben jihar Kaduna (KSIEC) ta sanar da sakamakon zaben kananan hukumomin da aka yi makon da ya gabata, inda ta tabbatar da sakamakon kujerun kananan hukumomi 18 cikin 23 da ke jihar.

Shugabar Hukumar zaben jihar Dakta Saratu Dikko, ce ta bayyana sakamakon da aka gudanar ranar 12 ga Mayu 2018, ta ce, jam’iyyar APC mai mulki ta samu nasarar lashe kananan hukumomi 14, yayin da jam’iyyar adawa ta lashe kujeru hudu.

Shugabar Hukumar ta ce, za a gudanar da sauran zabukan kananan hukumin biyar a ranar 2 ga watan Yuni 2018. Kananan hukumomin da APC ta lashe sun hada da: Birnin-Gwari da  Giwa da Igabi da Ikara da Kaduna ta Arewa da Sabon-Gari da Kagarko da Kubau da Kudan da Lere da Makarfi da Sanga da Soba da kuma Zaria, yayin da kuma jam’iyyar adawa ta PDP ta lashe kujerun kananan hukumomin Jema’a da Kachiya da  Kauru da kuma Zango-Kataf.

See also  Dr Usman Bugaje 2023: Jam'iyyar PRP Ce Mafita A Kasar nan

Jim kadan ta ce, sauran kananan hukumomin da za a sake zabukan su ne: Kaura da Jaba da Kajuru da Chikun da kuma Kaduna ta Kudu.

 

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here