YA GANAWA KARENSA AZABA DON YA KOYA MAI DARASI

0

YA GANAWA KARENSA AZABA DON YA KOYA MAI DARASI

An tsare wani mutum dan kimanin Shekaru 27 mai suna Patrick Shurod Campbell, saboda zarginsa na azabatarwa da cin zarafin zarafin karensa mai suna Dimitri.

Hukumar tsaro ta yankin Palm Beach County da ke Florida, sun bayyana cewa sun samu rahoton faruwar abun ne ta hanyar kiran waya daga makotan Campbell kan hayaniya da suka rika ji daga sashen da ya ke da zama.

Jami’an ‘Yansanda sun isa gidan na Campbell in da suka fara zantawa da makotansa kan batun, sun sheda masu cewa, sun rika jiyo hayaniya daga sashen Campbell da kuma karar karar, daga karshe ma bayan ya azabatar da shi sai ya harboshi waje kafin daga bisani ya sake kama shi ya kulle.

Bayan sun shiga dakin da Campbell ya ke sai suka rika jiyo zaurin Fitsari da warin kashi, in da Campbell ya sheda masu cewa Karen ya na cikin kewayen dakin, lokacin da suke kokarin balle kewayen sai Campbell ya fita daga dakin, bayan sun balle kyauren kewayen ne suka samu Karen kwance cikin duhu, sannan ya shiga cikin matsanancin hali jini na zuba a gefen kunnensa.

See also  YAN SANDA SUN SAKE KAMA MAHADI SHEHU

Campbell ya bayar da bayanin cewa, ya bugi Karen ne domin ya koya masa darasi, saboda bayan ya bar gida karen ya fito da ga inda ya kulle shi ya shiga dakinsa ya yi masa banna, shi ya sa ya daure karen ga wuya domin ya koya mashi darasi.

Ana dai tuhumar Campbell ne da laifin cin zarafin dabobbi, wanda hakan kuma ya sabawa doka, an dai sa ranar 11 ga watan Yuni domin cigaba da sauran karar.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here