MATASAN AREWA SUN RASA MADOGARA: MINTINA SHA BIYAR TARE DA IBRAHIM KATSINA

0

MATASAN AREWA SUN RASA MADOGARA: MINTINA SHA BIYAR TARE DA IBRAHIM KATSINA

Daga Abdulrahman Aliyu

A ranar Tara ga wannan wata ne, Babban jami’in gudanarwa na wannan jarida Malam Danjuma Katsina ya kira ni ta waya, yake sanar da ni cewa a kwai wani aiki da zan wakilce shi da za a yi Daura kasantuwar shi a ranar zai yi tafiya zuwa Abuja.

Awa guda tsakanin yin wayar da shi, wani ya kira ya shigo cikin wayata, bayan na amsa kiran ake sanar da ni cewa “Suna na Ibrahim Katsina Malam Danjuma ya bani lambarka ya ce na kiraka” kasan tuwar dama na san da maganar sai na amsa masa da cewa tabbas ya sanar da ni.

Karfe goma da rabi na ranar Tara ga watan Mayu 2018 na isa gidan Alhaji Ibrahim Katsina, domin ya yi man bayanin yadda aikin zai kasance.

Duk da kasancewar ya haifene, amma wani abun burgewa shi ya fito ya tarbemu sannan ya shigar damu falonsa muka zauna.

Bayan mun gaisa ne ya fara yi man bayanin dalilin da yasa suka shirya wannan taro karkashin wata cibiya da shi ne babban mai gudanarwa na cibiyar mai suna *Peace Builders Security Concept*
In da ya nuna mana cewa, sun lura cewa an yi matasa nisa a al’ummar Hausawa kuma babba abin da suke so shi ne matasan Hausawa su yi gogaggaya da sauran matasan Duniya a fuskar cigaba da sanin ciwon kai. Ya bada Misali da cewa ko jaridun da basa Kasuwa a arewa na Kudu duk suna magana ne kan cigaba, sabanin Jaridun mu na arewa da kullum mafi Yawan Kanun Labarinsu “an kashe mutane kaza…. An kai Hari wuri kaza… Wani ya yi wa wata fyade….” Da sauransu. Babu wani abu na kimiya ko wani abu na cigaba da za a kawowa matasa.

Mun tattauna da shi kuma kan yadda mutane ke samun dama da sunan Jihar su amma basa iya yiwa Jihar kome, sai dai kashe matasan ta. Ya bayyana mana cewa irin damar da ya samu da sunan Jihar Katsina ba zai taba bari ta tafi hakanan ba tare da ya sakawa Jihar ba, shi ya sa suka shirya wannan gangami wanda zai wayarwa matasa kai kan Illar shaye-shayan miyagun kwayoyi da kuma daba da Kauranci, wanda ya ce suna daga cikin abin da ke dankwafe tunanin Matasa ya kasance basu da tunanin kome a rayuwarsu.

Ya kara jaddada mana cewa irin yadda wasu baragurbin ‘yan siyasa ke amfani da matasa wajen cimma manufarsu babban abin takaici ne, da ya kamata ayi yaki da shi.

A cikin minti sha biyar din da muka yi muna tattaunawa ya tabbatar mana da cewa wannan Cibiya ta su zata cigaba da shirya irin wannan gangami, sannan kuma suna maraba da matasa da su zo su bada gudimuwarsu wajen dawo da martabarsu, ya tabbatar da cewa wannan aiki da suka faro ba wai gurinsu ne su ci gajiyarsa yanzu ba, suna fatan ko bayan ransu a samu sauyi ta dalilin wannan yunkuri….

Alhaji Ibrahim Katsina dai tsohon ma’aikacin hukumar ta fararen kaya ne da ya rike babban mukami a hukumar kafin ajiye aikinsa. Yanzu kuma ya fada aikin al’umma na ganin an sauya tunanin Matasa zuwa turba ta gari..

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here