MATAR DA TA KASHE JAMI IN SHIGI DA FICi A KASAR SUDAN

0

YADDA AKA GANO WADANDA KE DA HANNU WAJEN KASHE JAMI’IN SHIGE DA FICE DAN NIJERIYA DA KE AIKI A SUDAN

Daga Abdurahaman Aliyu

Jami’an tsaron kasar Sudan sun yi bayanin cikakke kan yadda aka kashe jami’in shige da fice Dan Nijeriya Habibu Almu.

Jami’an sun bayyana cewa sun shiga wani yanayi na damuwa da tashin hankali bayan da aka sanar da su labarin kisan Habibu Almu.

A safiyar da aka kashe shi ne aka sanar da su, in da suka Isa gidansa suka tarar da shi ya she bakin kofar daki tsirara an daba masa wuka.

Bayanan Yansandan ya nuna cewa mamacin ya yi kokarin fitowa daga dakin bayan an soka masa wukar saboda sawun jini da suka gani a cikin dakin.

Jami’an tsaron sun fara binciken kwakwaf ne bayan da suka lura cewa wanda ya yi kisan yana da alaka ta kusa da wanda aka karshen, saboda ba bu wata alama ta karya wa ko balle kyauren dakin, wanda hakan ya nuna cewa ko dai shi mamacin ya budewa wanda ya yi kisan da kansa ko kuma shi wanda ya yi kisan ya na da makulli da ya bude dakin da kansa.

Kwamitin da ke gudanar da wannan bincike a Khartoum karkashin jagorancin Manjo Janar Abdul’aziz Awad sun damke mutane da yawa da suke zargi da kisan, daga cikin wadanda aka kama din harda dalibai guda biyar da ke karatu a Jami’a, wadanda ake zaton suna da alaka da mamacin.
Jami’an tsaron sun bayyana cewa sun samu takardun Fasfot na mutane da dama a gidan mamacin, kasancewarsa daya daga cikin jami’an da ke aiki a bangaren samar da Fasfot.

Jami’an tsaron sun samu wata waya kirar Blackberry wadda aka goge duk wata manhaja da ka iya taimakawa wajen gane muhallin da aka yi amfani da shi.

See also  Mutum Miliyan 151 suke amfani da Internet a Nigeriya

A gefe guda kuma Jami’an tsaron Riyadh sun karbe binciken suka maido shi hannusu karkashin shugabancin Birgediya Ali Mohammad Osman domin gano gaskiyar yadda abin ya faru, haka kuma sun shirya wani babban kwamiti da zai Binciki wadanda ake tuhumar a karkashin kulawar shugaban sashen bincike na Riyadh Lutanal Kina Hartham Abdulrahman tare da hadin guiwar Ma’aikacin bincike Laftanar Kanal Mohammad Abdul Hakimda kuma babban Jami’an tsaro Manjo Base Eddin.

A yayi gudanar da binciken sun gano cewa kiran karshe da mamacin ya yi, ya kira wata yarinya ce daya daga cikin daliban da aka kama da farko. Bayan an yi amfani da fasahar zamani aka bi kiran wayar da ya yi sai ka gano cewa Yarinya ta tafo daga Arkweet zuwa Riyadj, da aka cigaba da bi sai aka gano cewa a ranar ta zo har gidan wanda aka kashe din.

Wannan yarinya dai daliba ce a Kwalejin Canadian da ke Khartoum kuma Yar asalin Nijeriya ce, an haifeta a shekarar 1990 ta na zaune a rukunin gidajen Jaya da ke Albalabal tare da sauran Dalibai Yanmata wadanda suke zaune gida daya.

Haka kuma an kara kama wasu yan mata biyu da ake zargi da hannu wajen kisan.

Jami’an tsaron sun bayyana cewa wadda ake zargin ta yi awon gaba da wasu makdan kudade a dakin wanda ake zargin, kuma suna da wata alaka da musamman tsakanin sa da wadda ake zargin da kisan na sa.

Wannan bajinta da kwarewa da jami’an tsaron Sudan suka nuna abin a yaba masu ne, musamman yadda suka bayyana wadanda suka aikata laifin cikin kankannin lokaci.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here