YADDA DAN MAJALISAR KATSINA YA SHA MARI WAJEN SHUGABAN APC NA JAHA

0

YADDA DAN MAJALISAR KATSINA YA SHA MARI WAJEN SHUGABAN APC NA JAHA
Daga wakilanmu
Tun kwanakin baya akayi ta rade radin cewa shugaban APC na jahar Katsina Alhaji shittu s shittu ya faffalawa Dan majalisar jiha Mai wakiltar. Karamar hukumar Kurfi Mari.labarin ya dade yana yawo Amma ba tabbacin ya abin ya faru..me yasa a ina ya faru?
Wakilan Taskar labarai sunyi zuzzurfan binciken lamarin.inda suka yi magana da tabbatau da kuma ganau..Akan lamarin.
Binciken Taskar labarai ya gano cewa abin da ya kawo sabanin shine ana Cikin hayaniyar zaben fitar da shugaban nin mazabun unguwanni na APC shi Dan majalisar jahar..sai ya rika neman . shugaban APC da sakataren sa..na karamar hukumar su ta Kurfi.
Yayi ta buga masu waya suka ki dauk daga baya ya gano suna a wani ofis a gidan gwamnatin Katsina.. Don Haka ya nufi can a fusace.yana zuwa.ya iske su sai ya hau su da zagi na cin fuska saboda sunki daukar wayarsa
A Lokacin a kwai wasu jiga jigan APC na Kurfi a wajen a kwai kuma shugaban jamiyyar APC na jaha.shitu s.shitu.
Ganau yace sai shittu ya taso daga Inda yake zaune yace honourable bai dace ba..kamar ka..gaban mu gaban wadannan ka Rika yiwa wadannan shugaban nin jam iya cin fuska Haka.
Sai Dan majalisar ya juya kan shugaban jam iyyar shittu Shima aka ce ya dankara masa wata maganar Mai zafin gaske…ai Malam shittu da yaji maganar ta shige shi kuma bai iya dauke zafin ta kafin kace meh ..har ya ta masa Mari masu kyau guda uku.
Ganau yace bamu an Kara ba..sai kawai muka ji gau gau gau Nan Dan majalisan ya sunkuya zai kife kamar yadda ake kisan Yan dambe sai sauran wadanda ke wurin su kayi wuf suka Shiga tsakani
Shi dai Dan majalisar dan tsololo ne ba kwari gashi nan dai shi ko shittu s shittu gajere ne kicicciri kakkarfa gashi dirarre.don Haka ko a kallo baka hada su
Ganau yace .munyi wuf muka Shiga tsakani..Don tsoron..kar marin ya Kai Dan majalisar kasa ..bamu San me zai biyo baya ba.
Dan majalisar daga baya shine kuma ya Rika neman ya maganar zata mutu ta tsaya a dakin da ya Sha falla
Duk wani yunkurin Jin ta bakin Dan majalisar yaci tura..ganinshi ya wahala mun aika masa sakon wayar sau biyar ba amsa.
Munyi magana da kakakin majalisar Dokoki ta jahar Akan ko.majalisar zata dau wani mataki?Akan wannan da nata da ya Sha Mari?
Alhaji Nasiru zango..cewa yayi bai San maganar ba bai da kuma masaniyar da ko majalisar zata dau wani mataki.
Majalisar ta koma zaman ta .Bayan ta dawo hutu..har taci gaba da gudanar da ayyukan ta..Amma har zuwa rubuta labarin nan..Basu ce komai ba Akan maganar a bayyane.
Binciken mu ya tabbatar Mana duk Akan wannan zaben na unguwanni, wani Dan majalisar ma..ya. Hau wani dattijon.. siyasa a karamar hukumar su da bugu.Ganau yace ta baya ya Kai masa naushi da yake wancan Yana da zafin nama yayi maza ya kare…kafin kace meh sai ya Dan majalisar na Shirin Aron na kare

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here