Tarihin Marigayi Liman Muhammadu lawal, limamin Masarautar Katsina.
Allahu akbar! Yau makonni biyu cif da al’ummar jahar Katsina da ɗaukacin ƙasa baki ɗaya suka tashi da alhinin rasuwar babban lamamin masallacin juma’a na garin Katsina.
Liman Muhammadu Lawal ɗa ne ga limaman Katsina Muhammadu Ahmadu Rufa’i, Mahaifiyarsa kuwa mutunniyar unguwar sha’iskawa ce, kuma ɗiya ga Alƙalin Ruma na wancan lokaci.
An haife liman Muhammadu Auwal a gidan mahaifinsa dake unguwar jaji, wadda a yau ake kira unguwar liman.
An yayye shi a gidan kakansa dake sha’iskawa a cikin garin katsina, da ya tasa ya dawo wajen mahaifinsa inda ya soma karatun addini. Ya samu karatu a hannun mahaifinsa, har ta kai ga an keɓe masa ɗaliban da ya ke karantarwa sama da mutum ɗari biyar, daga baya sai mahaifinsa ya bar masa kula da baki ɗaya ɗaliban, iyaka ya fito ya karantar da masu ɗaukar ilmi ya koma a gida.
Liman Muhammadu Auwal ya ɗauki ɗawainiyar karantarwa mahaifinsa baki ɗaya daga safe zuwa rana da bayan sallar azuhur zuwa la’asar da kuma bayan sallar Isha’i zuwa sha ɗayan dare. liman ya kan koyar da ɗalibansa a karance da kuma a zahirance kamar yadda liman ratibi na yanzu Malam Ɗayyau liman ya shaida wa jaridar taskar labarai, liman kan sa a ɗebo ruwa dan koyar da yadda akd alwala a zahirance da yadda ake aiwatar da salla dan kiyaye yadda take da yadda ake yin ta.
Duk da yawan ayyukan liman Lawal, bai hana shi zuwa neman ilimi ba, a wajen wasu malaman, ya kan je unguwar Madawaki wajen Malam Ali Ƙaramin Turmi dan yin darasu a allonsa, inda ta kai har ya samu kimanin sauka huɗu a wajensa. Haka kuma, ya yi karatun ilmi wajen shahararen malamin nan da aka ji ɗuriyarsa a ko’ina Malam Ala tsohuwar kasuwa da karutun fikihu a wajen ƙanan malam Ala wato Malam Yusuf. Kazalika, ya yi karatu wajen malam Hamisu mahaifin Alhaji Aminu Tireda dake unguwar Galadanci a cikin garin Katsina, sannan ma ya leƙa Darma wajen Malam Falulu dan yin karatun Nahuwu da lugga da kuma wajen Malam Muhammadu Kalipha tun yana Galadanci har ya koma ƙwalan ƙwalan yana zuwa ɗaukar karatu a wajensa. liman lawal ya kuma yi karatu wajen malam Ɗahiru wanda ya zo daga Makka ya sauka a unguwar alƙali dake cikin garin katsina.
Bayan gwagwarmayar neman ilmin da bayar da shi, limam liwal ya zama Ratibi bayan rasuwar mahaifinsa, liman Ahamadu Rufa’i, inda aka bai wa ƙanan mahaifinsa, Malam Abdulƙadir Limancin babban massalacin juma’a na masarautar katsina, daga baya liman Abdulƙadir ya baiwa ɗan yayyansa wato liman lawal jagorancin sallar juma’ah, bayan rasuwarsa sai mai martaba Sarkin Katsina Alhaji Muhammadu Kabir Usman ya naɗa liman Lawal babban limamin masarautar katsina aka kuma bai wa Malam Halliru ratibi, bayan rasuwarsa aka baiwa sabon liman na yanzu Ratibanci.
Babban liman masallacin juma’ah na masarautar katsina, shi ke jan ragamar duk wasu ayyukan na addini a majalissar sarki, da kuma jagorancin majalissar malamai na masarautar katsina. Da gabagar da sallar juma’a da sallar idi sallar roƙon ruwa da sauransu.
Duk da dai bamu samu ainahin rana da watan haifuwar marigayi liman Lawal ba, amma Ƴan uwansa sun bayyana ya rasu yana da shekaru sama da casa’in ya rasu ya bar ƴa’ƴa 27 maza 16 mata 11 da kuma matan aure guda huɗu, da ƴan’uwa da dama, an yi jana’izarsa a ranar da ya rasu da misalin ƙarfe huɗu, an kuma rufe shi a maƙabartar ɗan’takum inda duban jama’a suka raka gawarsa, zuwa kushewa, tare da mai martaba Sarkin Katsina Alhaji Abdulmumini Kabir Usman da mataimakin Gwamnan jahar katsina da sakataren gwamnati da manyan Malam daga ciki da wajan ƙasar na.
Bishir Suleiman
Jaridar Taskar Labarai