Game da Sabon Limamin da Masarautar katsina ta Naɗa.
Babban limamin juma’a na masarautar katsina, liman Almusɗafa wadda ake wa la’aƙabi da liman Gambo ƙane ne ga marigayi liman Lawal.
An haife shi a gidansu dake unguwar liman ya tashi a gaban mahaifinsa wadda ya zamo jagora a neman ilmansa, ya yi karatu mai zurfi a wajen mahaifinsa da kuma yayansa marigayi liman lawal, har ya samu hadda Al’kur’ani mai girma da sauran litattafan ilmi da dama, kuma yana karantar da ilmi a gidansu.
Liman Almusɗafa ya kasance ratibi a wajen yayansa liman Muhammadu lawal, bayan rasuwarsa, sai mai martaba Sarkin Katsina, Alhaji Abdulmumini Kabir Usman ya tabbatar da jagorancin limanci ga Malam Almusɗafa a ranar talata 6/5/018 a lokacin da Shugaban Ƙasar Najeriya Muhammadu Buhari ya ziyarci su a fadar mai martaba Sarki domin yi masu ta’aziyya, an kuma naɗa shi a ranar juma’ah 11/5/018 da misalin karfe shaɗaya na rana.
Mai martaba Sarkin Katsina, ya naɗa liman Almustafa a gaban ƴan majalissarsa da kuma ƴa’ƴa da ƴan’uwa na limamin.
Liman Almusɗafa ya karɓi dukkan ayyukan marigayi liman, da ya ke jagoranta a fadar.
Amma ya baiwa ɗan’uwansa alhakin jagorantar tafsir, wanda ake gudanarwa a duk shekara a tsohuwar fadar mai martaba sarkin na Katsina, bayan ya gudanar da tafsir na farko na wannan wata na Ramadan a fadar.
Ya baiwa Malam Ɗayyabu Liman jagoranci gudanar tafsirin, wanda ake karatun Sawi, kuma Tafsirin na gudana tare da masu jan baki guda uku, ɗaya na jan matanin Al’ƙur’ani mai girma, ɗaya na jan tafsarin sawi ɗayan kuma na jan kissa.
Liman Almusɗafa a halin yanzu yana da Matan aure uku da ƴaƴa 17 goma maza, shidda mata. Allah shi taya riƙo ya kuma jiƙan tsohon liman, amin.
Bishir Suleiman
Jaridar Taskar Labarai.