ME SOLOMON DULONG KE YI A OFISHIN MINISTAN MATASA DA WASANNI?
Daga Abdurrahman Aliyu
Ministan Matasa da Wasanni, a Nijereya babban Minista ne da ake ganin
duk wanda ya samu kujerar a kwai rawar da zai iya takawa domin ganin
matasan kasar sun samu cigaba da kuma daidaito hakkokinsu da ke hannun
gwamnati. Sanin kowane cewa Nijeriya kasa ce da matasa suka fi
rinjaye, kuma su ne suka taka muhimmiyar rawa wajen ganin wannan
gwamnatin ta dore.
Tun bayan da wannan gwamnatin ta ayyana Dan gwagwarmayar nan Solomon
Dulang a matsayin Minista Matasa da wasanni na kasar nan, matasa suka
rika murna da nuna goyan bayansu gare shi dari bias dari, musamman
saboda yadda aka sanshi da tsage gaskiya da kuma gwagwarmayar ganin
talaka ya samu ‘yancinsa a wannan kasa, ta kai cewa duk inda ya je
sai matasa syun yi cincirodo suna nuna masa goyan baya. Ita kanta
gwamnatin da farko har daga wuya take tana ganin ta bayar da mukami
inda ya dace, ga wanda zai fito da matasa daga halin da suke ciki, ya
kuma kawo cigaba ga kasar musamman ganin yadda matasa suka jajirce
wajen tabbatuwar wannan gwamnatin.
An fara hango wannan ministan a tebirin mai shayi ta runfunan masu
kosai yana tsayawa shan shayi da cin kosai wai kamar yadda yake a da
kafin ya samu mukamin ya na nuna cewa shi Kwamared ne, amma a zahirin
gaskiya wannan abu duk yaudara ce da farfaganda irin ta gwamnatin APC.
Duk wanda ke kasar nan ya zuwa yanzu in ka ce mashi ya gano maka
wannan minister ka bashi aiki, domin tuni shi ma ministan ya rikide
daga gwagwarmayar al’umma zuwa gwagwarmayar aljihu, domin duk wasu
ayyuka da yakamata ace matasa sun gani a kasa ta dalilin ofishinsa
tsit ka ke ji. Babu wani cigaba da matasan Nijeriya suka samu a
dalilin nada wannan dan gwagwarmaya matsayin minister, a bangaren
wasannin ma, an bar wannan kasar baya a fagagen wasanni da dama.
Wani abu mamaki shi ne yadda wannan minista ya ke neman ya rigide daga
ministan wasannin zuwa ministan kare Muradan Gwamnati, domin an fi jin
duriyarsa wajen mayar da raddi fiyer da ayyukan da aka dora masa
nauyin aiwatarwa.
Ya kamata Ministan Matasa ya fito ya yi ayyukan da aka dora masa na
sauya tunanin matasan kasar nan da kawo masu cigaba, musamman yadda
matasa suke da rauni a fagen neman sana’a da yadda za su iya juya kudi
ba wai yadda za su zama ‘yan maula da bangar siyasa kamar yadda salon
tafiyar Ministan ke nunawa a yanzu.
Ya kamata Minista ya sani duk wasu nauye-nauye da suka shafi matasa na
qarqashin ofishinsa, musamman tashi tsaye wajen yaki da sha tare da
fataucin miyagun kwayoyi, ya kamata ya sani sanya Jar hula ba tare da
aiki da aikidun jar hular ba aikin banza ne, kuma bas hi ke nuna mutum
dan gwagwarmaya ba ne ko dan neman yanci.
Minisata ya sani hakkin ofishinsa ne tashi tsaye na ganin an magance
yawan aikata laifuka wanda mafi yawanci matasa ne ke aikata su,
sakamakon rashin alkibla da suke fuskanta. Babu ko shakka bahaushe ya
yi gaskiya da ya ce in kana son kasan cikakken halin mutum to bashi
kudi, nan ne zaka gane waye shi, a da mun dauka duk babatu da Soloman
Dulong ke yi da gaske ne, kuma ya na kishin talakka, amma ana bashi
wannan mukami sai muka lura da cewa kurace da fatar akuya, wato dai
duk karya ce.
Rashin samun jajirtacce a wannan Ma’aikata ta matasa da wasanni ba
karamin koma baya ya jawo wa wannan gwamnati ba, domin da an fuskanci
matasa an dora su bias alkiblar da ta dace da hakan bata faru ba,
musamman a rika shirya masu wasu taruka da za a basu ilimi da kuma
wayar da kansu kan abin da ya shafi cigaba a duniya, amma wannan
minista ya yi burus abin sa sai fantamawarsa ya ke yadda ga dama.
Muna kira ga wannan minista da ya cire jar hularsa ya bari sai bayan
ya sauka sannan ya maida ta domin, a yanzu bata da wani amfani a
wajensa, a bangaren gwamnatin tarayya kuma ya kamata su rika gyaran
fuska ga kujerun da basu da wani amfani ga al’ummar kasa musamman irin
kujerar Ministan Matasa Wasanni domin gaskiya matasan wannan kasa basu
san amfanin wannan kujera ba.
wannan binciken naku ya yi ma’ana, ya kamata wannan mutumen ya san abin da yake duba da yadda ya ke dan gwagwarmaya, a baya.