GWAMNATINMU TA YI NASARAR DAKILE MASU TAYAR DA KAYAR BAYA

0

GWAMNATINMU TA YI NASARAR DAKILE MASU TAYAR DA KAYAR BAYA

Shugaba Buhari…

A cikin jawabin da shugaban kasa Muhammadu Buhari ya yi a yau na ranar Damakuradiyya, wadda ta yi daidai da cikar Nijeriya shekar goma sha Tara jera na mulkin Damakuradiyya, shugaban ya bayyana irin nasarar da suka samu na dakile masu tayar da kayar baya cikin dan kankanin lokaci.

A cikin jawabin nasa, Shugaba Buhari ya tabo batutuwa da dama na irin sauye-sauyen da gwamnatinsa ta kawo cikin shekara uku, da kuma wadanda take burin kawowa nan gaba.
Ya yi magana kan yadda cikin shekara uku aka samu ‘gagarumar nasara’ wajen dakile ayyukan masu tayar da kayar baya na Boko Haram, da ceto da yawa daga ‘yan matan Chibok da ‘yan matan Dapchi da wasu mutum 16,000 da ‘yan kungiyar suka sace, da kuma tabbatar da tsaro a sansanonin ‘yan gudun hijra.

Rikicin manoma da makiyaya
Shugaba Buhari ya tabo batun yadda ake samun karuwar rikice-rikice tsakanin manoma da makiyaya a jihohin kasar da dama, yana mai cewa al’amarin ba mai dadi ba ne, amma “gwamnati na iya bakin kokarinta don ganin an magance wannan matsala.”

Shugaba Buhari
Ya kuma tabo batun yadda gwamnatinsa ta samu nasara a yaki da cin hanci da rashawa, da samar da ayyukan yi da kuma bunkasa tattalin arziki.

Sai dai ana yawan sukarsa kan yadda gwamnatinsa ta kasa ciyar da tattalin arzikin kasar gaba, amma a jawabin nasa na yau Talata, ya ce duk da irin kalubalen da ake fuskanta, a yanzu tattalin arzikin na bunkasa.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here