KASASHE GOMA (10) DA SUKA FI ‘YAN DAMFARA A DUNIYA

1

KASASHE GOMA (10) DA SUKA FI ‘YAN DAMFARA A DUNIYA

Daga Abdurrahman Aliyu

Damfara a wannan zamani ta zama ruwan dare game duniya, sakamakon hanyoyin damfarar da aka samu kala-kala, kama tun daga na zamani har zuwa wadanda ake amfani da yanar gizo domin a damfari mutane. A wani bincike da jaridar Wanderslist ta yi, ta fito da wasu kasashe guda goma wadanda suka fi hadari a fagen damfara a duniya.
Wannan yasa Jaridar Taskar Labari ta yi nazarin wadannan kasashe domin ganin ko ya gaskiya lamarin ya ke.
1. Najeriya: ita ce kasa ta farko a duniya da ta fi yawan madamfara a Najeriya ne za a turo ma sakon ta waya cewa BVN dinka ta samu matsala a baka lamba ka tura bayanin asusn ajiyarka, kafin kyafatwar ido an kwashe maka kudi. A Nijeriya ne za a aiko maka da sakon cewa wai mace c eta gaji kudi dayawa wajen mijinta kuma ya mutu saboda haka tana sonka, da zaran ka amince zata bukaci asusun ajiyarka domin turo kudi sai dai kaji wayam kawai. Baya ga wadannan hanyoyin damfarar akwai hanyoyi da yawa musamman na kasuwanci da ake damfarar mutane a Nijeriya, hart a kai ga cewa kasashe da yawa basu amincewa ‘yan Nijerya wajen hudda das u saboda yadda suka kware wajen damfara, a Nijerya takai ga har gwamnati ‘yan kwangila ke damfara inda za su saida wa gwamnati wasu kayyaki na jabu, kuma haka za a tafi ba tare da daukar mataki ba. Irin wadannan halaye ana ganuin cewa ba wata kasa a duniya da ta kai Nijera Damfara.

2. Indiya: ita ce qasa ta biyu a duniya da ta fi mutane madamfara, bincike ya nuna cewa ba zai taba yiwuwa ka ziyarci kasar Indiya ba adamfareka ba ko jaraba damfarar ka, domin ko me tasi ka hawo da niyyar ya kai ka wani hotel mai sauki sai ya damfareka ta hanyar kaika mai tsada, wanda acen din za a fitar mashi da kamashonsa, haka ma a hotel din sai an damfareka. Duk abin da zaka saya Indiya in ba ka yi takatsantsan ba sai an damfareka, za a iya sayar ma abu na jabu ba tare da kasani ba, ko kuma a ka sayi abun mai kyau a damfareka a maida shin a jabu.

3. Chana: Kasa ta uku da aka fi samun madamfara a Duniya, saboda kwarewa da ke garesu kan hanyoyin kimiya shi yasa damfara a Chana ta zama ba kome ba, domin duk yadda ka kai ga wayo da hikima ana iya damfaraka, a Chana ne aka samo nau’in damfarar amfani da kananan yara domin a nuna marayu ne a damfari al’umma. A Chana ne ake amfani da wata na’ura a bakin ATM a samu bayanin ma’ajiyar mutum a kwashe mashi kudi.

4. Brazil: kasa ta hudu da suka kware da damfara a Duniya, a Brazil ana amfani da kyawawan ‘yanmata domin damfarar mutane, wannan abun ya bayyana kuru-kuru a shekarar 2016 lokacin da aka yi was an Olympics a kasar, an samu korafe0korafe na damfara da garkuwa da mutane ta amfanin da kyawawan ‘yanmata, wannan kiyasin ne ya sa kasar ta zama ta hudu wajen damfara a Duniya.

See also  Iyayen Yara Sun Bukaci Tinubu Ya Hana Kara Kudin Makaranta

5. Pakistan: kasa ta biyar da ked a hadari a bangaren damfara a Duniya, wannan ya faru ne saboda yadda jami’an tsaron kasar suka gurbata, hart a kai ga cewa mafi yawan damfarar da ake samu a kasar daga jami’an tsaro ce ake samunta, musamman ta kafafen sada zumunta na zamani, inda zasu yaudari mutum har vya kulla alaka da su amma daga karshe su yaudare shi, sannan a cen ne aka kware da sanyawa kwamfutar mutum ko wata na’ura ta shi bayaros, a nemi day a bayar a gyara bayan da gangan aka sanya mashi ita domin a damfare shi.

6. Indoesian: Kasa ta shidda da aka kware da damfara a duniya, tun a shekarar 2000 ake samun korafe-korafe na yadda ake daukar bayanan asusu ajiyar mutane na boge ana kwashe masu kudi, an sha samun yandamfara suna amfani da na’urar daukar bayanan asusun mutane ta boge suna kwashe masu kudi, wanda wannan na daya daga cikin dalilan da ya sa aka sanya kasar cikin jerin kasashen da suka fi ‘yan damfara.

7. Venezuela: Tun bayan da kasar ta fada cikin matsin tattalin arziki, ayyukan sdamfara suka baibaye kasar, musamman karancin ayyukan yi ga matasa da sauran tsadar abubuwan masarufi, wannan ya jefa kasar cikin halin damfara da cutar mutane domin a samu abin masarufi.

8. South African: A shekarar 2015 hukumar UJ Center for Cyber Security suka ayyana kasar a matsayin kasar da aka fi damfarar mutane ta bangaren asusun ajiya na banki, domin in dai mutum bai yi taka tsantsanba a South Afrika ba abu ne mai wahaka ba a damfare shi ta hanyar amfani da asusun ajiyarshi na banki ba. Wannan ya sa aka ayyana kasar cikin kasashe goma da aka fi damfarar mutane a Duniya.

9. Philippines: ita ce kasa mai lamba ta tara a duniya wajen damfarar mutane, domin a kasar ne mutum zai zo kai tsaye ya nuna cewa ai ya sanka, ya girmamma ka, amma a zahiri da kun kebe zai damfareka ya yi gaba, kuma dama karya yake bai sanka ba. Haka kuma a kasar ne ake hada kai da direbabin daukar kaya ana damfarar masu kayan da hanyar sauya fasalin kayandaga na ainahi.

10. Romania: Tun bayan faduwar daular Kwaminasanci kasar ta fada cikin talauci, shekaru da dama kasar na fama da masu damfara a kafar sadarwa da zamani, wanda hakan yasa kasar ta fada cikin damfara ta wannan kafar da kuma cutar mutane. Talauci ya taimaka sosai wajen damfara a kasar ta yadda za a kirkiri abu na boge a saida ma sai ka tafi ka gane cewa na boge ne.

Wadannan su ne kasashe goma da suka fi damfara a duniya, an fitar das u ne ta la’akari da korafe-korafen damfara da ake samu a kasar da kuma yadda duniya ta ke kallon salon damfara a kasashen.

1 COMMENT

 1. Da wane sikeli ko kuma bincike aka yi amfani wajen fitar da wannan jadsawali?
  Gaskiya ko kadan bam yarda ba cewa wai Najeriya ce ta fi kowa ‘Yan damfara a duniya wai kawai don ana yin damfara ta hanyar amfani da sakon SMS.
  Kuna ina ne cikin satin nan aka yi satar da ta kasance daya daga cikin sata mafi girma a duniya a kasar Bangladesh?
  A Najeriya wane hacker ne aka taba samu da yayi ma bank irin wannan mummunan ta’adi?
  Kun manta cewa a kasashen, wadanda kuke tunanin sune suka ci gaba, damararsu ma ta wuce a yi ta gaba da gaba, sai dai ta hanyar amfani da internet?
  Ya kamata idan zaku rubuta rahoto Ku fara yin bincike kwa-kwaf a Kansa tare da samo hujjoji kwarara daga sahihan kafafe.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here