Bajintar Ɗan Cirani Tasa ya Gana da Shugaban ƙasar Faransa Emmanuel Macron

0
1102

Bajintar Ɗan Cirani Tasa ya Gana da Shugaban ƙasar Faransa Emmanuel Macron

An jinjina wa wani Ɗan cirani daga ƙasar Mali sakamakon kwazon da ya nuna wajan hawa wani bene da ke birnin Paris na Faransa, domin ya ceto wani karamin yaro da ya maƙale kuma yana gab da faɗowa daga bene hawa na hudu.

An dai yaɗa hoton bidiyon Mamoudou Gassama a shafukan sada zumunta lokacin da ya kubatar da yaron.
A cikin minti ɗaya ya hau ginin in da ya ɗauki yaron mai shekara huɗu, wanda wani makwabcin iyayen yaron ke riƙe da hannunsa domin kar da ya fado ƙasa.

Shugaba Emmaneul Macron na Faransa ya gayyaci Mista Gassama zuwa fadarsa a ranar Litinin, domin ya yi masa godiya, inda Ya bashi takardar shedar zama ɗan ƙasa tare da aikin kwana-kwana wato (Fire Service).

Da yammacin ranar Asabar ne al’amarin ya faru a wata unguwa da ke arewacin Paris.
Mista Gassama ya ce yana tafiya ne lokacin da ya ga jama’a sun taru a gaban ginin.
Ya shaida wa kafar watsa labarai ta Faransa watau BFMTC cewa, lokacin da ya ga yaron yana ta shilo a bene, “Ban tsaya yin tunani ba, nan take na yanke shawarar ceto shi.”
“Da na riƙe shi a hannuna, na yi masa magana kuma na tambayeshi; me yasa ka yi haka? Sai dai be ce min komai ba”.

‘Yan sanda na yi wa mahaifin yaron tambayoyi bisa zargin cewa ya bar ɗansa a gida ba tare da kowa ba, a cewar wata majiyar shari’a.
Ana kyautata zaton mahaifiyar yaron ba ta Paris lokacin da al’amarin ya faru.
Magajin garin Paris Anne Hidalgo, ta jingina wa matashin mai shekara 22, kuma ta ce ta kira shi ta waya domin ta yi masa godiya.
Ta kuma ce ya kamata dukkanin ‘yan ƙasar su yi koyi da abin da ya yi.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here