Yadda ɗan Katsina ke Shanawa a Legas.

0

Yadda ɗan Katsina ke Shanawa a Legas.

Hausawa kan ce ” arziki kashin ne tako shi ake yi”, tabbas kuwa wannan magana, ta yi dai dai da yadda rayuwar Arc. Malam Ahmed kabir Abdullahi ta ke a kurmi, domin kuwa yana daga cikin ƴan’ arewa da suka yi gamo da katar a kurmi, duk da kasancewar sa ɗan asalin jahar katsina, amma bai hana shi, samun damar taka rawar ba, a cikin gwamnati jahar legas ba.

Dan ya yi gamo da katar da samu muƙamin shugabantar hukumar kula da ingancin samar da ruwa ta jahar, wanda mai girma gwamnan jahar ya ba shi muƙamin babbar mai gudanarwa na hukumar (LSWRC).

A lokacin da ake tattaunawa da shi, Arc Malam Abdullahi ya bayyana cewa ya daɗe da tsunduma cikin harkokin siyasar jahar legas inda har ta ka shi ga samun muƙami a ƙarƙashin gwamnatin gwamna Akinwunmi Ambode, inda ya sha alwashin tsara yadda za a samar da ingantaccen ruwa a jahar. Ba wai a rinƙa batun yaushe ya zo legas ko yaushe ya fara siyasa a jahar ba?

Ya cigaba da cewa shi tashin legas ne kuma haifaffenta, a unguwar Agege. Ya kuma halarci firamare da sakandire duk a cikin jahar ta legas, kafin daga bisani, ya samu damar shiga jami’ar Ahmadu Bello dake Zaria, inda ya samu digirin farko dana biyu kan kimiyar zane (Architecture)

Bayan ya kammala hidimar bautar ƙasa ya dawo legas inda ya fara aiki da kamfani ɓunƙasa kayayyaki, har ta kai ga ya riƙe babban manajan kamfanin.

Da sannun ya tsunduma a cikin siyasar yakinsa na Agege, inda ta kai har ya zama wakili a kwamitin kula da harkokin ilmi na ƙaramar hukumar Agege.

Har ila yau, Malam Abdullahi ya samu damar tsaya takarar kujerar mataimakin Ciyaman, a zaɓen ƙaramar hukumar ta Agege. A wajajen tsakiyar shekarar 1990 ya kuma samu nasara lashe zaɓen.

Haka kuma, ya samu damar yin aiki a wajajen shekarar 1996 zuwa 1997, kafin ya tsunduma sosai a cikin gwagwarmayar siyasa, wadda ya soma ta tun baya.

Kazalika, Malam Abdullahi ya samu kansa a cikin tafiyar jam’iyyar A.D in da ya marawa tsohon gwamnan jahar legas Asiwajo Bola Ahmed Tinubo baya, wanda a lokacin ya ke takarar kujerar gwamnan jahar, ya kuma samu nasarar zama gwamna, sakamakon
lashe zaɓen da aka gudanar wadda jam’iyyar tasa ta A.D ta tsayar da shi, a shekarar 1999 zuwa 2001.

Gwamna Tunubo ya janyo Malam Abdullahi a cikin gwamnatinsa, inda ya ba shi muƙamin Shuguban hukumar LASPEMA wato hukumar dake kula da tsaftace jahar legas, wannan muƙami ya ci gaba da riƙe shi har ya zuwa ƙarshen wa’adin mulkin tsohon gwamnan jahar legas Babatunde Fashola.

Malam Abdullahi har a yanzu ana damawa shi a cikin gwamnatin Akinwuni Ambode inda ya ke riƙe da muƙamin babban sakatare na hukumar tsarawa da kula da ingancin ruwa ta jahar legas.

Da ya ke zantawa da manema labarai, Malam Abdullahi ya bayyana cewa wannan ba ƙaramin aiki ba ne, gwamnan Ambode ya ba shi, dan haka ya sha alwashin cewa a shirye ya ke dan hidimtawa al’ummar jahar, ta tsara hanyar da za a samar wa sama da mutane miliyan ashirin ingantaccen ruwa a jahar, inda hukumar tasa ke aiki tukuru dan tabbatar da wannan ƙudiri nasa.

Da ya ke amsa tambaya dangane da ayyukan hukumarsa ta tsarawa da samar da ingantaccen ruwa da kuma takwararta ta samar da ruwan sha a jahar wato (LSWC).

Sai ya bayyana cewa ita hukumar samar da ruwan sha wato ( LSWC) aikin ta shi ne samar da ruwan sha a gidajen jama’a, ita kuwa hukumarsa da ya ke riƙo, aikinta kula da tsara yadda za a samar da ingantaccen ruwa a jahar, walau na rijiyoyi ko kuma famfon tuƙa tuƙa ga al’ ummar jahar.

A fanni da suka ƙware ke nan, wadda har ta kai hukumonin da abin ya shafa na duniya suka tabbatar da ƙwarewarsu ta hanya lura da ingantattun ayyukansu, da hukumar ke yi na samar da rijiyoyin burtsatse da kuma famfunan tuƙa tuƙa, da kuma ƙwarewa wajen samar da ingantaccen ruwa da kula da tsaftar ruwan leda, a jahar.

Da ya ke amsa tambaye shi, dan me jahar legas ta himmatu a wannan fanni na ruwa?

Sai ya kada baki ya ce ” Gwamnatin ta shafe dogon lokaci, tana wannan aiki, sai dai wannan gwamnati ta ƙara himmatuwa inda ta samar da dokar da ta shafi ɓangaren ruwa a jahar.

Ya cigaba da cewa hukumar samar da ruwa ta jaha tana ƙoƙari samar da kashi 33 bisa ɗari na ruwan da al’ummar jahar ke amfani da shi a rana, wanda haka ya haifar da yawaitar gine ginan rijiyoyi barkatai ba bisa ƙaida ba, wasu a kan gina su kusa da kwalbatai da masashe, wanda hakan ke haifar da gurɓataccen ruwa a jahar.

Hakan tasa, gwamnatin Ambode ta ƙudiri aniyar samarwa al’ummar jahar ingantaccen ruwa ga mazauna yankuna dabam daban na jaha.

Kazalika, da ya ke tofa albarkacin bakinsa dangane da batun tasirin siyasar ƴan arewa mazauna kurmi. Inda ya bayyana cewa ba ƙaramun tasiri ƴan Arewa mazauna kurmi ke da shi ba, a siyasar legas, don mutane masu haɗin kai da kishi da yin magana da murya ɗaya. Haka ya basu damar damawa da su a cikin al’umuran siyasar jahar. Ba lagas kaɗai ba, har da jahohin ogun dama yankin kudu maso yamma baki ɗaya, dan saboda kyakkyawan tsari na shugabanci da suke da shi, dan haka ake suke shiga cikin harkokin gina al’ummah na yankin.

Ya ƙara da cewa, yana alfahari da jahar legas dan ta zama gida a wajensa, a nan aka rufe mahaifinshi, a Agege, duk da kasancewarsa bakatsine, dan ba inda ƙasa ba ta kai mutum.

Malam Abdullahi ya yi godiya ga Allah, da yasa mutanan arewa mazauna legas, bisa ga yadda suke marawa gwamnati mai ci yanzu baya, wadda yasa a kullum jam’iyyar APC ke ƙara samun nasara tare da ɗumbin magoya baya.

Da ya ke amsa tambayar dangane da yunƙurin sa, na samun tikitin tsayawa takarar gwamnan jahar katsina, amma haƙar sa bata cimma ruwa ba, inda Alhaji Aminu Bello Masari ya samu.

Sai ya bayyana cewa, haka Allah ya nufa. Dama Alhaji Aminu Masari ne, Allah ya nufa da samun tikitin tsayawa takara a jam’iyyar APC kuma na mara masa baya matuƙa dan na fahimci ya daɗe yana fafutikar tsayawa takara, har kuma ya kai ga samun nasarar zama gwamnan jahar Katsina.

Kuma ina sa ne da irin ƙoƙarin da gwamnatinsa ke yi wajen ciyar da al’ummar jahar gaba, amma duk da haka har yanzu wasu na sukar gwamnatin, amma ina shawarartar da su ƙara haƙuri, akwai tsare tsare da dama da gwamnati ke da ƙudurin aiwatarwa don ci yar da jahar gaba.

Wanda lokaci ne kawai zai tabbatar da wannan ƙuduri, na cika alƙawuran da aka yi wa jama’a.

Bishir Suleiman
Jaridar Taskar Labarai

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here