ME YA KAI WANI JIGO A GWAMNATIN KATSINA HUKUMAR EFCC?
Daga wakilanmu.
Wani bincike da jaridar Taskar labarai ta gudanar ta gano.cewa wani jigo a gwamnatin APC ta Katsina an ganshi a ofishin EFCC dake Kano ranar 24/ mayu/ 2018.. majiyar Taskar labarai ta gano cewa Jami in da aka gani Wanda Mai karfin fada aji ne A gwamnatin..yaje ofis din ne Bisa gayyata da hukumar ta EFCC ta yi masa.
Majiyar ta Taskar labarai ta tabbatar da cewa..Jami in ya kwashe awoyi a cikin ofishin kafin ya fito ya tafi.
Majiyarmu ta tabbatar da cewa..Jami in ya sake komawa ofishin hukumar a cikin satin da ake ciki.
Mutumin ( Wanda muka sakaya sunansa har sai min kammala binciken mu). Ba a da tabbas me ya Kai shi ofishin hukumar..yaje ne..Bisa radin kansa..Koko yaje bin bahasin wasu koke wadanda gwamnatin Katsina ta APC ta kai tsohuwar gwamnatin PDP.. ko ko yaje ne Akan korafi da ake zargin an Kai akansa?! Bamu samu tabbacin me ya Kai shi ba.
Koma dai minene.. jaridar Taskar labarai na bin diddigi kuma zata kawo maku bayanin komai da dumi duminsa.