SHUGABA BUHARI YA RATTABA HANNU AKAN DOKAR DA TA BA MATASA DAMAR TSAYAWA TAKARA

0

SHUGABA BUHARI YA RATTABA HANNU AKAN DOKAR DA TA BA MATASA DAMAR TSAYAWA TAKARA

Daga Abdurrahman Aliyu

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya rattaba hannu akan dokar da ta baiwa Matasa damar tsayawa takara a fagen siyasar wannan kasa, an dade ana fadi tashin ganin an sanyawa wannan doka hannu kasancewar tun shekarar da ta wuce majalissun kasar nan suka rattaba hannu kan dokar.

Shugaban dai ya yi ikirarin sa hannun kan dokar tun a wurin jawabin da ya yi na ranar Damakuradiyya.

Ita dai wannan doka zata bayar da dama ga matasa ‘yan shekara 35 tsayawa takarar Shugaban kasa, sai kuma masu shekaru talatin damar tsayawa takara gwamna, haka kuma zata bada dama ga masu shekaru 25 damar tsayawa takara kujerun Majalissu na kasar nan.

Wannan doka dai matasa sun yi na’am da ita dari bisa dari, abin da ya rage sai a zura ido aga alfanun da wannan doka zata yi ga wannan kasa.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here