GWAMNAN JIHAR KATSINA YA BUƊE MASALLACIN JUMA’A A MAKARANTAR HASSAN USMAN KATSINA
Daga Abdurrahaman Aliyu
Rt. Hon. Aminu Bello Masari, a yau 1 ga watan Yuni, 2018 ya buɗe masallacin juma’a a makarantan kimiya da fasaha wadda akafi sani da Hassan Usman Katsina Polytechnic.
Gwamnan ya isa masallacin kafin fara sallar juma’a inda aka gudanar da sallar juma’a raka’a biyu tare da shi.
Wanda hakan ke gwada cewa an buɗe masallacin.
Masallacin juma’ar, zai amfani dubban musulmi wanɗanda suka haɗa da ma’aikatan da ɗaliban makarantar, kai har da sauran al’umma da suke kusanci da makarantar.
A lokacin buɗe masallacin, mai girma gwamna ya yi kira tare da fatan haɗin kan al’ummah musulmi baki ɗaya ba tare da banbancin aƙida ba domin kowane masallaci wuri ne na bautan Allah.
Daga ƙarshe ya kuma yi kira ga al’ummah musulmi baki ɗaya su kasance ‘yan uwan juna da ƙaunar juna, suyi kira tare da wa’azin da zai gina kyakkyawan fahimta tsakanin al’umma.
Daga Abdurrahaman Aliyu