BUHARI YA MAIDA RANAR DAMOKURADIYYA 12 YUNI MADADIN 29 MAYU DOMIN KARRAMA ABIYOLA

0

BUHARI YA MAIDA RANAR DAMOKURADIYYA 12 YUNI MADADIN 29 MAYU DOMIN KARRAMA ABIYOLA

Marigayi Abiola ne ya lashe zaben da akayi a watan Yuni na 1992 wanda gwamnatin mulkin soja ta wancan lokacin ta soke shi, kuma akasarin ‘yan kasar na ganin shi ne zabe mafi sahihanci a tarihin siyasar kasar.

Shugaba Buhari ya ce zai bai wa marigayin babbar lambar girmamawama ta GCFR a ranar bikin tuna wa da ranar a mako mai zuwa, kamar yadda wata sanarwa mai dauke da sahannun shugaban ta bayyana.

Hakazalika ya ce daga bana ranar 12 ga watan Yunin ce za ta zama ranar demokradiyya a kasar kuma ranar hutu a fadin kasar, maimakon ranar 29 ga watan Mayu.
Sai dai bai yi karin haske ba game da ko hakan na nufin an sauya ranar mika mulki ga sabuwar gwamnati, wanda ake yi duk bayan shekara hudu a ranar 29 ga watan Mayun.

See also  Gwamnatin Taraiyya Zata Kashe Naira Bilyan 24 Wajen Samar Da Hanyoyin Sadarwa A Filayen Jiragen Sama Da Kasuwanni Da Kuma Jami'oi

Har ila yau ya ce zai bai wa Ambasada Baba Gana Kingibe, wato mutumin da ya tsaya a matsayin mataimakin shugaban kasa tare da Abiola, lambar girmamawa ta GCON.

Hakazalika za a bai wa marigayi Gani Fawehinmi wato wani babban lauya wanda ya yi ta fadi tashi game da ranar tunawa da zaben 12 ga watan Yuni.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here