RICIN KUDI A KUNGIYAR MAWAKAN APC: AN KORI SU YALA DA NINGI.
Satin da ya wuce ne wata badakala ta barke tsakanin mawakan jam’iyyar APC, inda suka zargi cewa gwamnatin APC ta bayar da kudi ga Kungiyar kimanin naira miliyan dari a hannun fitaccen mawakin nan Rarara, shi kuma ya yike kudin ya ki basu har ma a wata waka da masu zargin suka fitar sun bayyana cewa ya koma kauyensu ya gina Filin kwallo da kudin.
A zargin da ake daya daga cikin ‘yayan kingiyar Haruna Ningi ya bayyana cewa Rarara ya kira shi ya fadi mashi cewa gwamnan Zamfara Abdulaziz Yari ya basu Naira miliyan 60 za a cika masu sauran kudin, amma har kawowa sadda ya yi jawabin ya bayyana cewa Rarara bai masu maganar kudin ba.
Abun ya kara zafafa ne bayan da Jaridar Damakuradiyya ta bayyana wani rahoto wanda ya nuna cewa, Ibrahim Yala ya ce ya gana da gwamanan Zamfara a Saudiya kuma ya fadi mashi cewar ba Miliyan dari da hamsin ya ba kungiyar ba Miliyan dari ba.
Jaridar Taskar Labarai ta samu wani kofin Odiyo Wanda Rarara ke karyata wannan zance inda ya nuna cewa sam bai san da maganarba, kuma shi ba a bashi ko Sisi ba, a cikin Odiyon mai minti goma Rarara ya bayyana cewa shi ba karamin mutum ba ne, kaf din mawakan da ke cikin tafiyar ba wanda zai kira ya ki zowa, kuma ya bayyana cewa shi ba wai dan shi ya kafa kungiyar ba, domin shi duk Gwamnan da ya tunkara dole ya bashi kudi, sun yi kungiyar ne domin su taimaki kananan mawaka, su hada su da gwamnoni.
Ya bayyana cewa wannn abun da ya faru na iya sanyawa gwamnan da ya yi niyar taimakonsu ya fasa.
Wannan badakala dai ta kai ga zartar da hukunci ga mutanen da ake zargi ta hannunsu ne wannan abun ya faru, daga cikin su akwai Haruna Aliyu Ningi wanda kungiyar ta kore shi bisa zargin cewa ya fice daga jam’iyyar APC ne ya koma jam’iyyar NNPP kuma har ya yi wakoki yana zagin APC din.
Sai Kuma Ibrahim Yala wanda shima kungiyar ta koreshi saboda ta na zarginsa da hada duk wasu kulle-kulle da suka faru a kungiyar.
Haka kuma kungiyar ta dakatar da wasu jerin mawaka bisa zargin tsoma baki a cikin badakalar mawakan sun hada da:
Jamilu Jadda Garko
Isyaku Muhammad Forest
Ahmad Kaka
Jamilu Darmanawa
Jamilu Roja.