Buhari Na Yunkurin Kamani Bisa  Zargin Boge: Obasanjo

0

Buhari Na Yunkurin Kamani Bisa  Zargin Boge: Obasanjo

Daga Abdurrahaman Aliyu

Tsohon Shugaban Kasa, Cif Olusegun Obasonjo ya koka kan cewa Shugaba Muhammad Buhari na shirin damke shi a kan zargin rashawa na karya.
Wannan ikirari na Obasonjo yana zuwa ne bayan makonni da shugabannin biyu suka yi musayar kalamai masu zafi.

Obasanjo ya Bayyana cewa,

“Wadansu majiyoyi na tsaro sun tabbatar min da cewa gwamnati na shirin amfani da hukumar EFCC da wasu shaidun boge domin kama ni da kuma tsare ni na din-din-din,”

Wannan zargi na kunshe ne a wata sanarwa da mai magana da yawun Mr Obasanjo, Kehinde Akinyemi, ya fitar a birnin Abeokuta ranar Juma’a, wadda kafafen yada labarai suka wallafa.

See also  AUREN SHUGABAN KASAR NIJERIYA JANAR YAKUBU GOWON 1969.

A kwanaki ne Shugaba Buhari ya zargi gwamnatin Obasanjo, wanda ya mulki kasar a matsayin zababben shugaba daga 1999 zuwa 2007, da kashe dubban daloli kan wutar lantarki ba tare da an ga wutar a kasa ba.

Sanarwar ta ce wasu majiyoyin tsaro sun yi zargin cewa Mr Obasanjo na cikin jerin sunayen mutanen da suke farauta, kuma rayuwarsa na cikin hadari.

Sanarwar ta kuma ce “Bayanan sun nuna abubuwa guda gwamnati na son amfani da hukumar EFCC domin sake bude bincike kan ayyukan gwamnatin tsohon shugaban ta hanyar amfani da bayanai da shedu na karya.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here