MATSALAR RUWAN SHA A JIHAR KATSINA ME GWAMNATIN MASARI KE YI?
daga Abdurrahaman Aliyu
Ya zuwa yanzu za a iya cewa matsalar ruwan sha a jihar Katsina ta zama ruwan dare game duniya. Wannan ya sa daya daga cikin wakilin Mu na wannan Jarida Abdurrahama Aliyu ya yi mana Rangadin Kananan hukumomin jihar Katsina guda 34 domin kalatawo da kuma yi mana duba kan irin matsalolin da kanan hukumomin ke fuskanta dangane da rashin ruwan sha da ake fama da shi.
Zamu rika tsakuro maku rahoton har zuwa lokacin da zamu kammala.
Duk wani wanda ya ziyarci karamar hukumar Katsina ko kuma cikin birnin Katsina zai ga irin yadda ake fama da matsalar ruwan sha, sakamakon yadda zaka rika ganin layin masu kura ana ta hidimar daukar ruwa.
Duk da cewa a birnin Katsina a kwai unguwannin da ke da wayarin na ruwan famfo amma shi kamsa ruwan famfon ana shafe kwana hudu zuwa biyar ba maido shi ba, wasu unguwannin kuma sai a shafe sama da wata guda ba a maido ruwan ba.
Tun da wannan gwanatin ta hau babu wani sabon wayarin da ta yi a unguwannin da ke cikin birnin Katsina, wannan ya haddasa matukar karancin ruwan a birnin duk da cewa gwamanatin ta na ikirarin gyarawa tare da fadada Dam din Ajiwa wanda shi ne ya kawo ruwa a cikin birnin.
Unguwanni da dama a birnin Katsina ruwa ya zama Gwal saboda tsananin wahalar sa da ake, amma gwanatin ta juya baya kamar bata san ana yi ba, Daga cikin unguwannin da ruwa ke kamshin Gwal a kwai.
Sabuwar unguwar Kofar Kaura
Abbatuwa
Yammawa
Filin folo
Makudawa
Tudun katsira
Saulawa
Kwalankwalan
Wani yanki na Daki Tara
Wani yanki na Kofar Marusa
Tudun Matawalle
Kwado
Sardauna Housing
Shagari lowcost da sauransu
Wani karin abin ban haushi yadda talaka ba ya iya gina rijiya a irin wadannan unguwanni saboda masu hannu da shuni sun riga sun gina rijiyoyin burtsatse a gudajensu, ta yadda ruwan ya yi kasa in ba karfi gareka ba ba zaka iya ginawa ba.
A karamar hukumar Rimi ma haka abun yake matsanancin wahalar ruwan sha ya dabaibaye garin dama cen garin baida cikakken wayarin Wanda yake samun ruwan famfo, matsalar ruwan sha a Rimi tayi kamarin da ko hukunci za a yi ma in aka kaika wasu kauyuka na Rimin matsalar Ruwan shan kadai ta ishaka hukunci, da ga cikin kauyukan akwai
Yakasai
Tokawa
Fardami
Yarmudi
Damisau
Yartsiya
Siyya
Kanya da sauransu
A wadanan garuruwan in ka debe famfunan burtsatse da ba su fi biyi ba su ne kawai mutanen garuruwan ke dogaro da su, Wanda hakan ke haddasa tafiyar mil da yawa wajen samo ruwan.
A karamar hukumar Jibiya duk da katafaren Dam din da ke garesu amma matsalar ruwan sha ta dabaibaye garin, binciken da muka yi ya tabbatar da cewa a cikin sati sai daya ake samun ruwan famfo a Jibiya shi ma kuma awoyi ne kawai.
Kusan duk kauyukan da ke Jibiya babbar matsalarsu ita ce ruwan Sha, misali kauyukan da ke fama da wannan matsala sun hada da:
Faru
Daddara
Daga
Kufan Daga
Magama
Kaware
Maitukuri
‘Yan nabasu da sauransu.
Batsari garin ne da ya sha fama da matsalar ruwan sha a baya, yanzu ma kuma abun ya dawo, domin irin yadda ruwan sha ya zama abin nema a Batsari ba karamin abin yashij hankali ba ne, a bangaren ruwan famfo ba ma ba a magaa domin ba ma wayarin dinsa balle a sa ran samu. A ranar Kasuwa bincikenmu ya tabbatar da ana sayar da jakar ruwa daya a kan naira 60.
Kauyukan Batsari suma kaf dinsu suna fama da matsalar tsaftattacen ruwan sha, da na amfanin yau da kullum.
Kurfi ma hakan abun ya ke matsalar ruwan sha ita ce tafi komi kamari a garin duk da kasancewarsu suna da manyan ‘yan siyasa da jami’an gwamnati amma matsalar ruwan sha ta zama abun tattaunawa a duk fadin kauyukan garin. Daga cikin fitattun kauyukan da ake fama da matsalar ruwan sha akwai:
Barkiya
Wurma
Tamu
Kaguwa
Koha
Hwadumawa
Bahirawa
Tsauri
Danfegi
Birchi da sauransu.
Charanchi ma haka abun ya ke matsalar ruwan sha ta zama abin da ta zama domin a Charanci akwai kauyuka da ake tafiyar kilo mita fiye da hudu domin samun ruwan sha. Daga cikin kauyukan da ke fama da matsalar ruwan sha Charanci akwai:
Kuraye
Sabon garin Kuraye
Yar’albasa
Banye
Safana
Radda da sauransu da dama.
Batagarawa duk da kudancin batagarwa da Katsina amma ana samun matsalar ruwan sha na tashin hankali a karamar hukmar Batagarwa, domin akwai garuruwan da gwara mutum ya baka hatsi da ya baka ruwa, saboda yadda ya zama Gwal a yankin. Baya ga Cikin garin Batagarwar Kans kauyukan da ke fama da matsalar ruwan a yankin suna da yawa, Wanda ba zamu iya tsayawa zayyanosu ba saboda yawansu. Amma ga kadan daga cikin su:
Bakiyawa
Tsanni
Tashar Bala
Morawa da sauransu .
Dutsanma su ma suna da ga cikin garuruwan da ke da katon Dam amma kuma suna fuskantar matsalar ruwa musamman ma kauyukan da ke zagaye da ita.
Kusan ba wani kauye a Dutsanma da ba ya fuskantar matsalar ruwa.
Kaita can dama baya kaita ta sha fama da matsalar ruwa musamman cikin garin Kaitar da wasu Kauyuka da ke yammacin kaitar.
Kauyuka irin su Yandaki da Riko da Radi da Jifatu da sauransu da dama duk suna fama da matsalar ruwan sha a gundumar Kaita.
Zamu cigaba
daga Abdurrahaman Aliyu