Dubban ‘Yan Gudun Hijira Daga Zamfara Sun Kwararo Jihar Katsina
Daga Abdurrahman Aliyu
A wani rahoto da Yusuf Ibrahim Jagaba na Rediyo DW ya gabatar ya bayyana cewa Sama da mutane 3000 ne suka shiga jihar Katsina neman mafaka daga jihar Zamfara a cikin makon nan sakamakon hare-haren yan bindiga.
Mafi akasarinsu suna zaune ne a runfunan kasuwanni a wani gari Dansabau dake karamar hukumar Kankara a jihar ta Katsina.
Wakilin DW Yusuf Ibrahim Jargaba ya halarci sansanin masu neman mafakar in da ya bayyana cewa,
“kusan wannan shi ne karon farko da aka samu kafa sansanin masu neman mafaka daga jihar Zamfara zuwa jihar Katsina bayan ‘yan bindigar sun fatattakesu daga garuruwan su yawancin wadannan ‘yan gudun hijira dai ta rayuwar su suke ba ta dukiya ba, domin dukiyoyin duk maharan sunyi awon gaba da ita.
Wadannan Al’umma dai sun yi sansani ne a runfunan kasuwa da ke garin Dansabau dake karamar hukumar Kankara a jihar ta Katsina”.
A zantawar da ya yi da wasu daga cikin wadanda abun ya shafa mai suna.
Shukurana Ibrahim wani matashi da ya sha da kyar bayan an harbesa a cikin da kuma hannu, ya bayyana cewa,
“Ni a lokacin da suka zo cikin gari sun same ni da ni da makwancina harma sun kasheshi ni kuma Allah ne ya sa mutuwa bazata afka dani ba wannan kuma harbi ne na farko a cinyata da ya harban da farko ya dauka na mutu na tashi tsaye in ruga sai naji na fadi sai ya karomun wani harbi ga hannu’.
An tambaye shi ko jami’an tsaro ko masu bada agajin gaggawa basu kawo masu dauki ba? Sai ya bayyana cewa,
“Har yanzu babu wanda muka gani daga cikin Gwamnatin jihar Zamfara da sunan su taimaka mana kuma yanzu haka mun fi mu dubu uku a nan”
Wata tsohuwa kuwa da aka kashewa ‘yaya da jikoki ta rika rusa kuka ta na bayanin halin da suke ciki.
“An kashe mun da kuma an hanamu zaman gari sannan an kwashe mana dukiya gashi duk mun yi shuka amma babu manoma”
Har yanzu da tsugunne bata kare ba domin kuwa maharan sun mamaye garuruwan wadannan mutane bayan da wasu su ka yi yinkurin komawa garuruwan nasu a cewar wannan matar da aka zanta da ita.
“Munja Awakin mu dan mu koma gidajenmu to mun tafi zuwa garuruwan mu sai mazajen mu sukace mu dawo ga Fulani nan sun yi sansani suna jira lokaci yayi”
Kawo yanzu dai babu wani tallafi da Gwamnatin jihar Zamfara ta yi wa wadannan Al’umma na ta baya ga tallafin da mahukuntan jihar Katsina su kai masu hakanne yasa na tintibi shugaban hukumar ba da agajin gaugawa na jihar ta Zamfara dan jin ko wane hali ake ciki kan wadan nan Al’umma, in da ya bayyana cewa,
“Yanzu haka mutanen mu na can wurin nasan sun tafi karamar hukumar Kankara”
Jihar zamfara dai na cigaba da hare-haren yan bindiga kusan kowanne mako wanda ke sanadiyar rasa rayuka da dukiyoyin Al’ummar da basu jiba ba su gani ba.
Shi dai wannan rikiji ba sabon abu bane a Jihar Zamfara, amma wani abun mamaki har kawo wa yanzu ba wani abun azo a gani da gwamanatin Jihar Zamfara ke gudanarwa domin mangance wannan matsalar.