Kotu a Najeriya ta Daure Tsohon Gwamnan Filato Joshua Dariye Shekara a16 a Gidan Yari

0

Kotu a Najeriya ta Daure Tsohon Gwamnan Filato Joshua Dariye Shekara a16 a Gidan Yari

Wata kotu Nijeriya ta samu Joshua Dariye da laifin cin amana da almubazzaranci.

Mai shari’a Adebukola Banjoko ta samu Mr Dariye, da laifi a kan tuhumce-tuhumce 17 daga cikin 23 da hukumar yaki da cin hanci ta EFCC ta zarge shi da aikatawa.

Laifukan sun hada da almubazzaranci da halatta kudin haram a lokacin da ya mulki jihar ta Filato na tsawon shekara shida da doriya tsakanin 1999 zuwa 2017.
Sanata Dariye ya kasance cikin damuwa da dimuwa a lokacin da ake karanta hukuncin.

Wannan hukunci na zuwa kwanaki kadan bayan da mai Shari’a Banjoko ta daure tsohon gwamnan Taraba Jolly Nyame shekara 14 a gidan yari saboda almubazzaranci da zamba da halatta kudin haram.

An yanke masa shekara 14 saboda cin amanar dukiyar jama’a, sannan shekara biyu saboda almubazzaranci da dukiyar gwamnati.
Za a hade hukuncin wuri guda, wanda hakan ke nufin zai yi zaman jarum na shekara 14. Kuma ba a bashi zabin biyan tara ba.

See also  Koyi Da Gwamna Masari Yasa Na Gina Hanyar Ruwa A cikin Unguwarmu

Mr Dariye ya yi shiru yana saurare a lokacin da ake karanta hukuncin a babbar kotun birnin tarayya Abuja da ke unguwar Gudu.
Mai shari’a Bamijoko ta ce Sanata Dariye ya barnatar da sama da naira biliyan daya da aka bai wa jihar domin shawo kan matsalar zaizayar kasa.
Mai shari’ar ta ce tsohon gwamnan ya fi jiharsa kudi, a don haka “babu wata hujja ta aikata cin hanci da rashawa ta kowacce fuska ga mai kudi ko talaka”.

Lauyansa Kanu Agabi ya soki sahihancin shaidun da aka yi amfani da su wurin samunsa da laifi, amma mai shari’ar ta ce shaidun sun tabbatar da almundahanar da aka tuhume shi da aikatawa.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here