SAI WATA RANA RAMADAN!

0

SAI WATA RANA RAMADAN!

Yau Laraba 28/09/1439 (lissafin Nijeriya) kuma 13/06/2018 da ƙarfe 5:36 na safe Wata zaya ɓullo a “Ƙafin Gabas” (Eastern Horizon); yayin da ita kuma Rana ta ɓullo da ƙarfe 6:03 na safe; watau mintuna 27 tsakaninta da Wata.

Bayan awa 3 da minti 9, Watan zaya ɓace gabaɗaya a sararin sama, yadda ba a iya ganin shi a ko ina cikin duniya daga bisa doron Ƙasa; watau kenan ya shin sake ɓullowa a gan shi a matsayin “Jinjirin Watan Shauwal”, in sha’Allah!

Bisa ga al’adar Wata, ya kan sake fitowa a matsyin “Jinjirin Wata” bayan ya faku da awa 13 da ƴan mintoci (aƙalla) ko kuma da awa 15 (akasara), bisa halin yanayin da ake ciki. Amma dai Masana falaki sunfi rinjaye a kan awa 15 ɗin.

Bisa la’akari da lokacin fakuwar Watan a yau (8:45) da safe, bayan nan awa 15 zata kama da ƙarfe 11:45 na daren ya laraba, dan haka bs za a ganshi ba a wannan sashe namu na duniya. Sai dai a lokacin fa, a wasu sassan duniya gari ya riga ya waye, Alhamis ta shigo har rana ma ta fito.

Wannan ƙididdiga na nuni ne ga cewa lallai wata na iya ganuwa a wannan sashe namu na duniya a gobe Alhamis, in sha’Allah! Idan Allah Ya sa an ga Watan Iydi zaya kama Juma’ah kenan.

Allah Ya nuna mamu lokacin da rai da ƙoshin lafiya cikin kwanciyar hankali, amin domin arzikin Annabi Muhammad,
صلى الله عليه وآله وصحبه وسلم

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here