Gidauniyar Maigemu Ta Rabawa Marayu Kayan Sallah na Miliyoyin Nairori

0

Gidauniyar Maigemu Ta Rabawa Marayu Kayan Sallah na Miliyoyin Nairori4

Daga Abdurrahman Aliyu

Sama da Marayu dari biyar (500) ne suka amfana da tallafin kayan Sallah da gidauniyar Maigemo suka raba a garin Kankiya da ke Jihar Katsina.

Wannan gidauniya dai wadda take karkashin daukar Nauyin Dan majialissar Jiha mai wakiltar Kankiya Honarabul Salisu Hamza Rimaye, a yau 13/6/2017 ta shirya gagarumin taro na raba kayan sallah ga marayun da suka fito daga yankin wanda a tarihin karamar hukumar ba a taba samun wani dan siyasa ko mai kudi da ya taba kwatanta haka ba.

Taron ya samu halartar wakilan hakiman Kankiya da Rimaye da Shugaban kunguyar JIBIWIS na Kankiya da Babban limamin masallacin Juma’a na Kankiya da kantoman Riko na karamar hukumar Kankiya da kuma shugaban Bankin Bayar da Lamuni na tarayya Wanda ya samu wakilcin Alhaji Ashiru Magam, da sauran manyan baki da ga ko’ina na fadin Karamar hukumar Kankiya da wasu kananan hukumomin makwabtanta.

A lokacin da shugaban Gidauniyar ke jawabi ya bayyana cewa aikin wannan gidauniya ba wai ya tsaya ga tallafawa Marayu ba ne kawai, akwai bayar da gudumuwa ga marasa lafiya da kuma Samar da gurabun karatu da daukar nauyin karatun ga marasa karfi. Haka kuma gidauniyar ta na koyar da sana’o’i domin domin sanya matasa su dogara da kansu da kuma dakile zaman banza a cikin al’umma, sannan ya kara da cewa gidauniyar ta na daukar nauyin ayyuka na addini a kafafen sadarwa domin daukaka kalmar Allah.

A lokacin da wakilin Hikimin Kankiya ke jawabi ya nuna cewa a tarihin Kankiya ba a taba samun wani Wanda ya yi irin wannan aiki ba, saboda haka masarautar Kankiya da ta Rimaye suna cikin wannan Gidauniya tsundum kuma , kuma suna fatan sauran Al’umma su yi koyi da irin wannan gidauniya domin a tallafi Marayu a duk inda suke.

Shi ma Imam Musa Abubakar ya bayyana cewa saboda muhimmancin taimakon Marayu a cikin Kura’ani aya Tara tayi magana kan Marayu, kuma mafi yawancin ayoyin suna magana ne kan a tallafi marayun.

Yayi matukar yabawa wannan gidauniya saboda irin wannan jan aiki da ta dauko na taimakon Marayu, sannan ya yi addu’a ga Wanda ya assasa wannan Gidauniya fatan Allah ya taimake shi kan dukkan abin da ya sa gaba a rayuwa.

Sannan an yabawa wadanda suka zabo wadannan Marayu saboda namijin kokarin da suka yi ba tare da nuna wariya ba ko bambancin jam’iyya.

Bayan kammala taron an raraba kayan ga Marayu sama da dari biyar daga shiyoyi goma na Karamar hukumar Kankiya, wadanda kiyasin kudin kayan zai kai miliyoyin Nairori, sannan an bayar da kayan buda baki ga duk mahalarta taron.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here