Shekaruna 15 Ban Ga Shekau Ba – Inji Mahaifiyarsa

0

Shekaruna 15 Ban Ga Shekau Ba – Inji Mahaifiyarsa

Mahaifiyar Shugaban Boko Haram Abubakar Shekau ta tattauna da Muryar Amurka inda ta bayyana cewa ta yi shekaru 15 ba ta ganshi ba.

A kauyen Shekau da ke Jihar Yobe, dattawa da shugabannin al’umma sun kai Muryar Amurka wajen Falmata Abubakar wadda suka ce ita ce mahaifiyar Shugaban kungiyar Boko Haram, Abubakar Shekau. Mahaifinsa limamin kauye ne gabanin rasuwarsa a wasu ‘yan shekaru da suka gabata.

Falmata ta ce bata taba magana da ‘yan jarida ba kafin Muryar Amurka kuma ba ta masaniyar inda ya ke ko halin da ya ke ciki.

“Ko ya mutu ne, ko yana nan da ransa, ba ni da masaniya. Allah kadai ya sani. Shekaru na goma sha biyar kenan tun da na ganinsa,” inji ta.

“Tun da Shekau ya hadu da Mohammed Yusuf, ban sake ganinshi ba,” inji Falmata

“Na san dana ne, kuma kowa ya san son da uwa ke wa danta, amma halayenmu sun sha banban,” inji ta. “Ya jefa mutane da dama cikin bala’i. Ina ma zan ganshi domin in ja hankalinsa? Ya jefa jama’a da dama cikin tashin hankali, amma ina rokon Allah ya shirye shi.”

An ciro daga shafin sarauniya na Faceboo

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here