Sun Kashe Abokinsu Domin Su Yi Tsafi Da Zuciyarsa

0

Sun Kashe Abokinsu Domin Su Yi Tsafi Da Zuciyarsa

Daga Abdurrahaman ALiyu

Rundunar ‘Yansandan Jihar Legas ta cabke wasu mutane hudu da take tuhuma da laifin kashe wani abokin su domin yin tsafi da shi.

Daya daga cikin wadanda ake zargin mai suna Danial ya bayyanawa jami’an tsaro cewa, shi dan ainahin garin Chibok ne a Maiduguri, kuma su hudu ne suka taru suka kashe abokinsu mai suna Ishaiah James domin su yi tsafi da shi.

Ya bayyana cewa wani boka ne ya tsunduma su cikin wannan harka, domin su yi kudi daga sana’ar su ta Zamfara.

Bokan ya bayyana masu cewa ba a yin kudi haka nan dole sai mutum na da ilimi, sun tambaye shi me ne ne mafita? Sai ya umurce su da cewa za a samo zuciyar mutum sai ayi masu tsafin da za su samu kudi. Ya kuma umurce su da su bada naira dubu Dari, take suka bashi dubu sittin da alkawarin za su cika mashi dubu arba’in.

Bayan kwana kadan da faruwar haka, sai bokan ya kirasu ya sanar da su cewa, Wanda ya tura ya samo mashi zuciyar mutum din ‘yan banga sun harbe shi. Amma su na iya nemowa su kawo da kansu.

Sun shiga damuwa ta yadda za su samu wannan abu, sai shugabansu mai suna Audu ya ce ya na da mafita, in da ya basu shawarar cewa su gayyaci wani dan’uwanshi mai suna Ishiar Wanda aboki ne garesu, domin su kashe shi, dukansu suka aminta.

See also  Yan Ina Da Kisa Sun Kashe Mutane Biyar A Kauyen Giwa

Sun kira shi ta waya inda suka bukaci da ya samesu a Mashayar Ajah da ke nan Legas.

Da dare ya yi suka je mashayar suka hadu da shi, suka sha giya suka sai mashi doya.

Wajen karfe daya na dare suka ta shi suka tafi gida, a bisa hanyar su ne, Audu ya ce yana jin fitsari ya yi gaba ya shiga wani lungu rike da wuka a hannunsa domin yin fitsari, baki dayan su suka yi Sauri suka isa lungun, inda Ishiar na karasowa wani daga cikinsu ya buga mashi wani abu akai ya fadi, Audu ya burma masa suka a kirji, Ayuba ya sa hannu ya fara laluban zuciyar, amma bai samo ta ba, sai da na amshi wukar na bubbuda wajen sannan muka ciro zuciyar.

Bayan mun kaiwa Bokan zuciyar a Ijebu Ode sake Jihar Ogun sai ya amsa inda ya dafa ta tare da wani wake, ya ce da munci wannan waken manyan kudi zasu shigo mana kuma duk abinda muka tunkara sai mun samu. Sanna ya bukaci da mu cika mashi dubu 40 dinsa.

Wata Mata da ta gansu tare a Daren da zasu kashe shi, ta bayyana cewa ta kadu matuka da taji ance ya mutu, saboda a ranar tare ta gansu kuma dukkansu garin su daya wato Chibok a Jihar Maiduguri.

Jami’an tsaro na cigaba da farautar Bokan wanda ya arce.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here