Wasan Crotia da Nijeriya: Darasussa Guda 5 Da Muka Koya A Ciki

0

Wasan Crotia da Nijeriya: Darasussa Guda 5 Da Muka Koya A Ciki

Daga Wakilinmu Yaseer Kallah

Ba wani abin mamaki a cikin sakamakon wasan da aka buga tsakanin tawagar kwallon kafar Nijeriya da ta Croatia da aka buga a yammacin ranar Asabar, inda kasar Crotia ta samu nasara kan takwararta ta Nijeriya.

An jefa kwallaye guda biyu a cikin wasan, wanda bai yi wani armashi ba, inda dan wasan kasar Croatia, Mario Mandzukic ya zamo sila a cikin dukkan kwallaye guda biyun da aka jefa cikin ragar Nijeriya.

Cin gida da Oghenekaro Etebo na tawagar Nijeriya ya yi shi ne ya zamo kwallo ta farko da aka fara jefawa bayan rabin sa’a da take wasan, inda Mandzukic na tawagar Crotia ya kafa wa kwallon kai izuwa ragar Nijeriya. Cikin rashin sa’a kwallon ta bugi kafar Etebo sannan ta baude cikin ragar Nijeriya.

Bayan nan kuma, Troost-Ekong dan wasan baya na Nijeriya ya jawo bugun fenarati izuwa ragar Nijeriya sakamakon kokowar da ya yi da dan wasan gaban Croatia. Cikin rashin sa’a kuma golan Nijeriya ya gaza ture kwallon.

Domin kokarin tsira da kwallayen da ta jefa, Croatia ta yi kokarin rufe bayanta a cikin sauran mintuna 20 din da sukai saura. Hakan ya sa suka sauka kasa tare da ‘yan sauye-sauye domin kara kange ragarsu.

Bayan sakamakon wasan, me kuma ka gano game da wasan wanda aka buga ranar Asabar?

An ciro daga shafin sarauniya…

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here