HUKUMAR KWASTOM SUN TSARE ALHAJI AMINU BUSH

0

ALHAJI AMINU BUSH…NA TSARE A HANNUN KWASTAM
Daga Muazu Hassan
Matashin nan dake tashe wajen fiton Kaya..daga kasar Nijar zuwa Nijeriya.. Alhaji Aminu bush…..yanzu Haka Yana tsare a Abuja a wajen Jami an kwastam , kamar yadda jaridar Taskar labarai .ta tabbatar…
Binciken da Taskar labarai suka yi, sun gano tun kwanaki baya jami an kwastam.. sukayi Masa wayo..da cewa yazo Abuja Domin. Bada wani bahasi…Yana Shiga sai kawai suka Sakaya shi.
Jaridar Taskar labarai.sun jiyo cewa.ana binciken sa ne Akan wata takardun korafi da wasu suka rubutawa kwastam…suka ce ..yanzu shine shugaban Yan sumoga na yankin Arewa maso yamma.a takardun korafin aka ce yanzu. A wajen fiton Kaya shine ya maye kwafin.. Alhaji Dahiru Bara u mangal
Wanda masu korafin suka ce ..ya bar harkar yaja baya da ita.ya maida karfi a wasu harkokin sa na samun kudi.inji takardar korafin na wasu da suka rubuta
Jaridar Taskar labarai..ta jiyo cewa..Kwanturolà na kwastam na kasa kanar Hamid Ali shine ya bada umurnin kamo shi Aminu Bush kuma yake sa da Ido da tsaron nasa ..
Jaridar ta gano cewa.duk kwanakin nan Yana tsare ne ba a ce Masa uffan ba..sai a wannan satin aka fara daukar jawabin shi..
Jaridar ta gano Aminu bush na da kyakykyawan alaka da Jami an kwastam..Wanda ya Sanya ake mamakin ya Haka ta faru a gare shi.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here