KUJERAR MATAIMAKIN GWAMNA A MATSAYI DA TSARIN MULKIN NAJERIYA
Daga Danjuma Katsina.
Wani bincike da na gudanar akan wannan matsayi na kujerar mataimakin gwamna shine matsayine wanda sai mai hakurin gaske da kai zuciya nesa ke iya rike ta. Sai kuma wanda ke d a wata irin fahimta da dangantaka mai karfin gaske tsakanin mai rike da ita da kuma gwamnan da suke mulki a tare.
Kujera da matsayi ne wanda tsarin mulkin kasa ya kasa bata ko mai ita wani hobbassa sai dai kawai cewa .in gwamna baya nan ka rike. Shima wannan ba dole bane in gwamnan yaga dama yana iya baiwa wani ba kai ba. sai kuma duk wani aiki da gwamna ya baka.
A tsarin mulki a matsayin baka da hus na wani abu da zaka iya aikatawa. Sai abin da gwamnanka ya baka. baka da ikon bada umurnin fitar da kudi ko da kuwa ficika ce. In dai ba daga cikin aljifunsa zai fitar ba.
Wannan matsaya ya sanya masu rike da wannan matsaya sai ka samu suna fama da jama ar da suke karkashinsu a siyasance. Suna tsammanin cewa saboda matsayin da suke rike dashi na suna daga gwamna sai su. Don haka suna tsammanin duk yadda gwamna ya fantama dole ne su fantama a hakan
A wani lokaci idan mai wannan matsayi yace zai rika kula jama ar na siyasa sai kaga yan tsurku sun fara kai suka ga gwamna cewa lallai mataimakin nasa yana masa wata makarkashiya ko yana shirya msa zagon kasa baka Ankara sai kaga an fara yakin sunkuru da gaba in ba akai zuciya nesa ba . sai kaga mataimakin gwamnan ya zama abin tausayi.
Irin wannan sarkakkkiya wanda mataimakin gwamna kan shiga shi yasa a baya akayi ta samun masu rike da matsayin a baya sun rika kira a soke kujerar, wanda ya fara wannan kiran a baya shine Alhaji tukur jikamshi lokacin yana mataimakin gwamna .zamanin marigayi umaru musa yar adua. Da aka shiga tsakaninsu sai da Alhaji tukur jikamshi ya zama abin tausayi
Irin wannan sarkakkiya da matsala ya sanya ake samun rigingimu tsakanin gwamnoni da mataimaknsu a jihohi daban daban ,kamar misali kwanan nan a kano tsakanin ganduje da farfesa hafiz wanda aka ruwaito mataimakin na wasu zantuttuka ga mutanensa. Har yana cewa ba a sake tsayawa takara tare dashi ba. da abin day a faru kwanan nan a Bauchi inda mataimakin ya ajiye yace gode da damar da aka bashi,da yadda ya taba faruwa lokacin bafarawa na gwamna wammako na mataimaki a jahar sokoto..
A karkashin kasa jihohi da yawa na fadan sari ka noke tsakanin gwamnansu da mataimakansu kuma da yawa suna cin dudduniyar juna,wannan ya sanya gwamnoni da yawa basu son suga cewa mataimakansu sun gaje su. Wasu na cewa misalai da aka samu na mataimaka na gadar gwamnoni . in sun hau sukan kokarin rama cutarwar da aka yi masu lokacin suna biyayya. A sokoto da wammako ya zama gwamna said a ya hana bafarawa sakat a siyasance haka da mamuda ya zama gwamna said a ya hana yarima sakat a jahar zamfara. Ga abin dake faruwa yanzu a jahar kano tsakanin kwankwaso da Ganduje,
Kujerar mataimakin gwamna wani matsayi ne na iya ruwa fitar da kai.in kuma bakayi taka tsantsan ba. to zaka shiga rububi don gwamnanka zai kuble ka kuma baa bin da zaka iya a tsarin mulki
Sai dai a ganka da yawan jami an tsaro da jiniya in kana so .wadanda suma tsarin mulki ne ya baka su. Amma a ciki ba komai sai fankam fayam.domin hakkinka na ofishin iya wanda doka ta baka ,in baka basu iya rike maka danginka balle siyasarka .kamar yadda binciken da nayi ya tabbatar mani.
Wani mataimakin gwamna day a samu matsala da gwamnansa ya shaida mani cewa.da gwamnansa ya rike masa komai saboda munafukai sun shiga tsakaninsu.yace sai da cefane irin wanda ya kamata ayi a gida na ya nemi ya gagare ni.’’inji shi
Kamar yadda nace , matsayin iya ruwa ne fitar da kai, idan ka amsa dole kasan matsayin da tsarin mulki wanda ba komai bane da ya wuce bin abin da gwamnanka keso. Daga nan ya zaka zauna da mukarraban gwamna lafiya kamar yadda wani tsohon mataimakin gwamna ya shaida mani .’’ zaka yi ta gani da ji daga wajensu[jami an gwamna]kuma ba ruwansu da kai don haka sai ka kai zuciya nesa’’
sai kuma ya zaka tafiyar da siyasarka ? wanda yafi wahalar sha ani da kuma tsaka mai wuya.in ka rika biya su da tara su. Da taimaka masu .a ce ma gwamna kana da manufar da ta sanya kake hakan in akai nasarar hada ku fada.na lahira sai fika jin dadi,in kuma ka kyale mutanenka ace ka watsar dasu anan wani yanayi ne na gaba kura baya siyaki.
Rashin wani takaimemen matsayin da tsarin mulki ya baiwa kujerar ya sanya idan kuna dasawa da gwamnanka sai baka wata ministiri yaceka rika kula da ita, sannan ya rika baka wasu hukumomi yace kai ne shugabansu , ya kuma rika sanya ka kana jagorantar wasu kwamitoci. Duk wannan in wata matsala ta tashi gwamnan na iya kwace su cikin kyaftawa da basmallah. Kuma ba yadda zaka iya. Baka kuma da ta cewa
Wani tsohon mataimakin gwamna da nayi Magana dashi, ma anar kujerar sai yace ‘’ kujera ce ta biyayya ,wakilci, dan aike da kuma jiran me za a saka ,da aikata abinda aka ce ma kayi ,ya kara da cewa kujera ce ta hakuri da amfani da hikima ka zauna da kowa lafiya’’
Bincike na ya tabbatar mani wasu mataimakan gwamna za suyi ta hakuri,amma da an bar gwamnatin babu ruwansu da gwamnansu .don suna tuna cutarwa da gwamnan yayi masu. Nayi Magana da mataimakan gwamna biyu,wanda suke cikin wannaan koken . daya ya shaida mani cewa ‘ Duk halin da na shiga gwamna na ne ya saka ni sai fara kawo hujjojinsa.’’ Dayan kuma ya shaida mani cewa. ‘’ yanzu zaman kai na nake nayi biyayya a lokacin da muna gwamnati kamar yadda tsarin mulki ya bani to yanzu ba gwamnatin ! sai kuma in ci gaba da biyayya?ga wa”
In kaga dan siyasa a kujerar mataimakin gwamna abu uku yake nema wajen ka. Shawara, tausayawa, sai addu a.
Danjuma Katsina . mawallafi/ dan jarida ana samunsa a 08035904408 email .katsinaoffice@yahoo.com.twitter @danjuma katsina